Wata tankar mai ta yi bindiga tare da kamawa da wuta unguwar Sharada da ke Kano.
Lamarin ya faru da tsakar rana, lokacin da ake sauke mai a wani gida mai da ke Sharada.
Akalla mutum 51 su ka ji rauni sakamakon gobarar wadda ta tashi daidai lokacin da ake kwartsa rana.
Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano Garba Idris ya nuna matukar damuwa da tashin gobarar, kuma ya dora laifin a kan masu gidan mai din, saboda sauke mai da su ka yi ana tsakiyar zafin rana.
“Kowa ya san bai kamata ba, kuma doka ba ta yarda a sauke mai a gari kamar Kano a lokacin da ake kwartsa rana ba.
“Mun tabbatar da cewa lamarin ya shafi mutane 51 wadanda su ka ji raunuka, cikin su kuwa har da jami’an kashe gobara su takwai.”
Shugaban Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, Nura Maigari ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta binciki lamarin.