Fitacciyar ‘yar jarida Kadaria Ahmed ta karyata raderadin da wasu jaridu ke yadawa wai ita ma tana cikin wadanda gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi wa watandar filayen jihar.
Kadaria ta ce gwamnatin Kaduna ba ta mallaka mata kyautar fili ko gida ba a jihar. Duk da ko cewa a matsayina na ‘yar Najeriya, tana da damar ta mallaki fili ko gida a ko ina a fadin kasar nan, kamar yadda dokar ya ce.
” Ina so kowa ya sani, da farko dai ni a jihar Kaduna aka haife ni, amma kuma ko da na ga ya dace in mallaki gida a jihar ko fili, yadda kowa ke bi haka na bi don nima in samu fili a jihar.
” A farkon wannan shekara na rubuta takardar neman mallakin fili da gida a Kaduna bayan na ga sanarwar cewa duk mai bukata zai iya cika fom ya biya kudi a kuma mallaka mishi fili ko gida.
” Bayan na cika fom sannan na bi ta hanyar da kowa ya ke bi ba tare da na bi ta wata hanyar ba, na sanayya, ko kuma in canja suna don a bani ba. A haka ina zaune wasika ta iske ni cewa suna na ya fito cikin wadanda aka baiwa fili har guda biyu.
” Sai dai kuma kash, a takardar an bani fili ne mai darajar naira miliyan 25, kuma dokar gwamnati ta ce dole in biya kudin cif-cif cikin kwanaki 14.Haka nan dai na kurkurda na samu kashi 10 cikin 100 na biya gwamnati da zumman zan nemi cikon ko ta hanyar bashin banki ne kafin wadin ya cika. Amma kuma ban samu, daga nan sai na yi wa hukumar KADIS wasikar a kara min lokaci.
Kadariya ta ce har yanzu ba a aiko mata da amsar wasikarta ba sai daai ta ji an ce dokar gwamnati bai yarda a kara wa wani lokaci ba idan wa’adin ya cika, sannan kuma kudin da aka biya ba za a maido masa ba.
Daga nan ne na karkata zuwa ganin ko zan iya samun nasara a fili na biyu da gwamnati ta bani. Shima nan bayan na biya kudin filin sai aka ce dole in gina gidar cikin watanni 6 ko shekara daya idan ba haka ba na sai dai fa shima in hakura.
Duk da ina da burin mallakar gida a jihar da aka haifeni gashi kiri-kiri ya gagare ni.
Wannan shine gaskiyar magana, ba rahotannin karerayi da ake watsawa wa ba wanda ni ko ba haka bane.
Discussion about this post