Hukumar ICPC ta buga sanarwar farautar Tsohon Shugaban Bankin Bada Lamuni na Najeriya, Federal Mortgage Bank of Nigeria, Gimba Kumo.
Ana farautar Kumo wanda suruki ne ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da wasu mutum biyu bisa zargin su da hannu a harkallar dala miliyan 65.
Gimba Kumo ya auri diyar Buhari mai suna Fatima, a cikin 2016, a garin Daura, Jihar Katsina.
Hukumar ICPC ta buga sanarwar farauta da cigiyar Gimba Kumo, Tarry Rufus da Bola Ogunsola.
Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na ICPC, Azuka Ogugua, tare da cewa duk inda aka gan su, to a damke su.
Baya ga rattaba sunayen su, sanarwar ta kara da labta hotunan su baro-baro tare da kattaba adadin harkallar dala miliyan 65 da ake zargin su.
“Duk wanda ya gan su ya gaggauta kiran wadannan lambobin: 08031230280, 08031230281, 08031230283, 07056990190, 07056990191, ko kuma 080022554272.
Idan ba a manta ba, Kwamitin Binciken Kashe Kudaden Gwamnati na Majalisar Dattawa ya gayyaci Gimba Kumo dangane da yadda su ka biya wata kwangila ta naira biliyan uku sau biyu.
Discussion about this post