WURU-WURUN DALA MILIYAN 65: Gimba Kumon da ICPC ke farauta, yanzu ba surukin Buhari ba ne – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta musanta ikirarin da kafafen yada labarai su ka yi cewa Gimba Kumo da Hukumar ICPC ke neman kan wuru-wurun dala miliyan 65, yanzu ba surukin Shugaba Muhammadu Buhari ba ne.

Wata sanarwa da Kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu ya sa wa hannu, ta bayyana cewa labarin da aka buga cewa ICPC na neman surukin Buhari, hakan ya nuna cewa Gwmnatin Buhari ba ta yi wa hukumomin dakile zambar kudade katsalandan.

Shehu ya ce hakan ya nuna babu wani shafaffe da mai kenan a cikin Gwamnatin Shugaba Buhari.

“To sai dai kuma wani gyara a labarin shi ne yanzu Gimba Kumo ba surukin Buhari ba ne. A baya akwai alaka ta surukantaka tsakanin su, amma tun shekarun baya waccan igiya ta alaka ta surukantaka ta tsinke.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa ICPC ta buga gangar gangamin farautar surukin Buhari.

Hukumar ICPC ta buga sanarwar farautar Tsohon Shugaban Bankin Bada Lamuni na Najeriya, Federal Mortgage Bank of Nigeria, Gimba Kumo.

Ana farautar Kumo wanda suruki ne ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da wasu mutum biyu bisa zargin su da hannu a harkallar dala miliyan 65.

Gimba Kumo ya auri diyar Buhari mai suna Fatima, a cikin 2016, a garin Daura, Jihar Katsina.

Hukumar ICPC ta buga sanarwar farauta da cigiyar Gimba Kumo, Tarry Rufus da Bola Ogunsola.

Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na ICPC, Azuka Ogugua, tare da cewa duk inda aka gan su, to a damke su.

Baya ga rattaba sunayen su, sanarwar ta kara da labta hotunan su baro-baro tare da kattaba adadin harkallar dala miliyan 65 da ake zargin su.

“Duk wanda ya gan su ya gaggauta kiran wadannan lambobin: 08031230280, 08031230281, 08031230283, 07056990190, 07056990191, ko kuma 080022554272.

Idan ba a manta ba, Kwamitin Binciken Kashe Kudaden Gwamnati na Majalisar Dattawa ya gayyaci Gimba Kumo dangane da yadda su ka biya wata kwangila ta naira biliyan uku sau biyu.

A karshe Garba Shehu ya ce wasu kawai sun dai sa lakabin “surukin Buhari” ne a labarin farautar Gimba Kumo, don kawai su samu cinikin jaridun su.

Share.

game da Author