Wata ma’aikaciyar jinya Toyosi Ogunkunle ta bayyana cewa wanke hannu da ruwa da sabulu kariya ne daga kamuwa da cututtuka musamman cutar da ake kira ‘Gastroenteritis’.
Toyosi ta fadi haka ne a hira da tayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Juma’a a garin Ibadan.
Ta ce amfani da man tsaftace hannu wato ‘hand sanitizer’ na da kyau amma tsaftace hannu ta hanyar wanke wa da ruwa da sabulu ba.
” Man tsaftace hannu baya tsaftace hannu kamar yadda ruwa da sabulu zai yi domin shi hand sanitizer baya iya kawar da kwayoyin cutar gastroenteritis daga hannun mutum.
“Kwayoyin cutar gastroenteritis cuta be dake hadassa amai da gudawa
“Kwayoyin cutar Gastroenteritis ya fi kama yara kanana da kuma rashin tsaftace hannu.
Idan ba a manta ba Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta hori mutane da su daure da wanke hannaye a koda yaushe da ruwa da sabulu domin guje wa kamuwa da kuma yada cutar korona a kasa.
Hukumar ta ce baya ga kaucewa kamuwa da korona da wanke hannaye da ruwa da sabulu ke yi, yin haka na kare mutum daga kamuwa da cututtuka.
Alfanun wanke hannaye da ruwa da sabulu
1. Koya wa yara dabi’ar wanke hannuwa da ruwa da sabulu na kare su daga kamuwa da mugan cututtuka.
2. Mafi yawan mutanen Najeriya basu wanke hannayen su da ruwa da sabulu.
3. Ya zama dole a rika wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.
4. Wanke hannu da ruwa da sabulu na rage yawan mace-macen mutane.
5. Dole ma’aikatan kiwon lafiya su rika wanke hannayen su da ruwa da sabulu kafin da bayan sun duba marasa lafiya.