Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya Abubakar Malami, ya ƙaryata zargin da lauyan Ibrahim Magu kuma tsohon ɗan Kwamitin Ƙwato Kuɗaɗe Da Kadarorin Sata ya yi masa cewa ya yi wa Najeriya sagegeduwar da ta yi sanadiyyar kwamitin bai karbo dalolin sata har biliyan 60 da aka sata daga NNPC, aka boye a Texas, Amurka ba.
Kakakin Yaɗa Laabrai na Minista Malami, Umar Gwandu ne ya ƙaryata zargin wanda
Ojaomo ya yi wa Malami.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin lauyan Magu ya ce Minista Malami ya hana ƙwato wasu maƙudan daloli biliyan 60 da aka kimshe a Amurka
A labarin wanda PREMIUM TIMES HAUSA ta wallafa, lauyan na Magu ya zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami da shiga gaba ya hana Kwamitin Kwato Kuɗaɗen Sata ya ƙwato wasu kuɗaɗe har dala biliyan 60 daga Amurka.
Lauyan rusasshen Kwamitin Shugaban Kasa Mai Binciken Kadarorin Satar da aka Ƙwato, Tosin Ojaomo ne ya yi wannan zargin a ranar Laraba, a gaban Kwamitin Majalisa Mai Binciken Kudade da Kadarorin Satar da aka Kwato Hannun Barayin Gwamnati.
Haka nan kuma Ojaoma ya taba zama lauyan tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu a lokacin da Kwamitin Ayo Salami ke binciken Magu din.
Sai dai kuma duk da wannan ikirarin zargi da Ojaomo ya yi wa Minista Malami a gaban kwamiti, bai gabatar da wata shaida ko da ta fallen takarda ɗaya ba.
Wancan Rusasshen Kwamitin Shugaban Kasa dai Okoi Obono-Obla ne ya shugabance shi. Haka shi ɗin ma Obla ɗin ya fuskanci tuhumar karbar tishiyar baki da rashawa.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya rushe kwamitin cikin 2019.
Zarge-zargen Ojaomo Kan Minista Malami:
Ojaomo ya ce kuɗin da Malami ya kange ya hana karbowa, dala biliyan 60 ne da barayin gwamnati su ka sace daga NNPC, su ka kimshe a Texas, Amurka.
Ya ce Malami ya riƙa ti wa kwamitin su Ojaomo ɗin tarnaƙi da dabaibayi don kada su ƙwato waɗancan maƙudan biliyoyin daloli.
“Ya Mai Girma Shugaban Kwamiti, an ba mu rahoton sirri na wasu maƙudan daloli har biliyan 60 da aka sata daga NNPC, aka boye a birnin Texas na Amurka. Har mun fara yin nisa da bincike, amma sai Minista Malami ya dakatar da mu, ya ƙwace binciken ya maida a ƙarƙashin sa.”
Sannan kuma Ojaomo ya yi zargin cewa NNPC ta danƙare wasu daloli miliyan 223 a Polaris Bank, wai da sunan asusun gudanar da ayyuka.
“Kuma wannan asusu na Polaris Bank inda NNPC ya boye dala miliyan 223, ba a haɗa shi da Asusun Bai Ɗaya na Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ba.” Inji Ojaomo.
Sbugaban Kwamitin Bincike Adejoro Adeogun, ɗan APC daga Jihar Ondo, ya ƙyale Ojaomo ya ci gaba da lissafo zarge-zargen da ya ke yi wa Malami, duk kuwa da cewa wasu mambobin kwamitin sun nemi ya gabatar da hujjoji.
Wani Damfareren Zargin Jidar Naira Biliyan 10:
Ojaomo ya ci gaba da shaida wa kwamiti cewa kwamitin su wanda Shugaba Buhari ya rushe, ya samu labarin Akanta-Janar na Tarayya ya jidi naira biliyan 10 daga Asusun Hukumar Inshorar Ma’aikata (NHIS), kuɗaɗen da aka yi lodin jidar su sau biyu, wato biliyan biyar-biyar kenan.
“Yayin da mu ka gayyaci gayyaci Akanta Janar domin ya yi bayani, kuma mu ka aika as fam domin ya cike, ya yi bayanin kuɗaɗen da ya jida da kuma abin da za a yi da su, sai ya ƙi cika fam, ya ce ofishin sa ba a ƙarƙashin kwamitin mu ya ke ba. Wai zaman kan sa ya ke yi kamar yadda dokar Najeriya ta ba shi iko. Wannan bayanin a rubuce ya aiko mana shi.”
Daga nan dai da aka ga tone-tonen sun yi yawa, sai Shugaban Kwamitin bincike ya dakatar da Ojaomo, ya ce ya kawo wa kwamiti kwafe-kwafen hujjojin zarge-zargen da ya yi wa Malami da Akanta-Janar.
Sannan kuma kwaniti ya ce zai sake rubuta takardar gayyata d
ga Minista Malami.
Kare Zargi: Ƙarya Ojaomo Ya Shirga Min -Malami
Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Malami, Umar Gwandu ya ce duk wani zargin karbar kuɗaɗen sata ko hana-ruwa-gudu wajen karbo wasu daloli har biliyan 60 da ake wa Malami duk ƙarairayi ne.
“Malami na ƙalubalantar duk wani mai zargi ya gabatar da hujjoji a matsayin shaidar cewa ba ƙarya ya kantara ba, kuma ba sharri ya kitsa wa Malami ba.
“Kowa ya san kyakkyawar rawar da Abubakar Malami ya taka wajen ƙwato kuɗaɗen sata daga Amurka, Birtaniya da Tsibirin New Jersey. Kuma ba za a manta da dala biliyan 9 na P&ID waɗanda Minista Malami ya taka muhimmiyar rawa a kan su ba.
“Saboda haka da masu zargi da masu kantara ƙarairayi da masu sharri, duk su na yi ne don su bata wa Malami suna.” Inji Gwandu.