Wabba mai laifi ne, duk wanda ya gaya mana inda yake boye za mu saka masa da kudi – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna ya Nasir El-Rufai ya yi kira ha ‘Yan Kaduna su nemo masa shugaban kungiyar Kwadago Ayuba Wabba, cewa wai shi mai laifi ne.

El-Rufai ya rubuta a shafin sa ta tiwita cewa duk wanda ya fadi wa gwamnati inda Wabba ke boye za a bashi ladar kudi masu yawa.

Ya ce yajin aikin da Wabba ya kira a jihar Kaduna, ya saba wa doka, saboda haka gwamnati na neman sa a cafke shi, kuma duk wanda ya bada bayanan inda yake ko ya yi sanadiyyar aka kama shi za a bashi kyautar kudi mai tsoka.

Yau an shiga cikin kwana na uku a yajin aikin da ake yi a jihar Kaduna.

Share.

game da Author