VAT: Gwamnati ta tatsi harajin naira biliyan 496.39 daga Janairu zuwa Afrilun 2021 -NBS

0

Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FRIS) ta tara harajin naira biliyan 496.39 a cikin watanni hudu, daga Janairu zuwa Afrilun 2021.

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ce ta fitar da jadawalin yadda aka tara kudaden a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

Masana’antun cikin kasar ne su ka samar wa Gwamnatin Tarayya naira biliyan 49.4.

Sai kuma masu samar da ayyukan yau da kullum na wasu kwararru da ya samar da naira biliyan 42.50.

Ma’aikatu da Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnatin Tarayya sun tara naira biliyan 26.96 a cikin wata hudu.

A wadanda ke kutal, sahun baya wajen tara haraji sun hada da albarkatun kasa mai naira miliyan 48.36. Sai bangaren kayan saka da yadika da atamfoci naira miliyan 77.01 da kuma bangaren suturu naira miliyan 289.41.

Su kuma Ma’aikatar Kwastan ta Kasa ta karbi kudaden haraji na naira biliyan 99.88 duk a cikin watanni hudu na farkon shekarar 2021.

Harajin cikin gida na daga cikin kalilan na kudaden da Gwamnatin Tarayya ke hadawa da cinikin danyen mai ta na biyan kason kudade ga Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi.

Share.

game da Author