Uzor Kalu ya yi tofin Allah-wadai ga batagarin da su ka kai wa ofishin INEC hari a jihar Abiya

0

Tsohon gwamnan Jihar Abiya wanda kuma shi ne mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Dakta Orji Uzor Kalu, ya yi Allah-wadai da harin da wasu batagari su ka kai wa ofishin Hukumar Zabe ta Kasa na Karamar Hukumar Ohafia da ke jihar.

Shi dai ofishin na INEC, wasu wadanda ba a san ko su waye ba ne su ka banka masa wuta a ranar Lahadi, inda su ka lalata kayayyakin zabe da wasu kadarorin.

A yayin da ya ke bayyana harin da cewa ya saba wa tsarin dimokiradiyya kuma rashin wayewa ne, Kalu ya yi kira ga jami’an tsaro da su fara cikakken bincike kan harin don su gano wadanda su ka aikata wannan ta’asar kuma su gurfanar da su a kotu.

Ya nanata cewa tilas ne a kare tsarin mulkin dimokiradiyya na Nijeriya da ke tasawa domin a samu cigaba.

A lokacin da ya ke kira ga ‘yan siyasa da su rungumi kyawawan halayen dimokiradiyya a al’amuran su, tsohon gwamnan ya kuma nanata cewa ita siyasa ba a yin ta da nufin a mutu ko a yi rai.

Ya ce, “Harin da aka kai wa ofishin INEC na Karamar Hukumar Ohafia ta Jihar Abiya bai da wani hurumi kuma ba za a amince da shi ba.

Ya ce, “Hukumar zabe ta Nijeriya, INEC, ta na kokari wajen gudanar da muhimmin aikin ta na habaka tare da gina muradan dimokiradiyya a kasar nan.

”Masu daukar nauyi da masu aiwatar da wannan hari abokan gabar kasar nan ne.

“Ina kira ga hukumomin tsaro da su gano mutanen da su ka aikata wannan hari da nufin hana aukuwar irin sa a nan gaba.”

Kalu ya yi kira ga INEC da kada ta karaya wajen kokarin da ta ke yi na habaka muradan dimokiradiyya a Nijeriya.

Share.

game da Author