Kociyan Villareal Unai Emery dai har zuwa 2004, ɗan wasa ne a kulob ɗin Lorca Deportivo. Ana tsakiyar wasa aka ji masa rauni, wanda bai sake wasa ba, sai ya ci gaba da koya wa ‘yan wasan kulob din ƙwallo.
A wannan shekara da aka ji masa rauni, a wannan shekarar ce ya kai ƙungiyar Lorca Deportivo buga wasan La Liga na Spain a karo na farkon tarihin ƙungiyar.
Daga nan cikin 2005, sai ƙungiyar Ameria a Spain ɗin dai ta ɗauke shi koyarwa. Can ɗin ma a shekarar ya kai Almeria ga buga gasar La Liga a karo na farkon tarihin ƙungiyar.
Daga nan kuma sai Valencia ta ɗauke shi. Kuma a shekaru uku a jere Valencia ta riƙa fitowa gasar Champions League, inda a La Liga Valencia ta riƙa yin na uku ba sau ɗaya ko sau biyu ba.
Emery ya koma Sevilla, inda ƙoƙarin sa ya kai ƙungiyar ga ɗaukar Kofin Europa sau uku a jere, tarihin da wata ƙungiya ba ta taba yi a gasar Europa ba.
Ya koma ƙungiyar PSG ta Faransa, inda ya ci kofi har guda bakwai daban-daban. Cikin su har da kofuna hudu da ya ci a cikin kakar wasa ɗaya tal.
Ya koma Arsenal inda a can ma ya kai wasan ƙarshe a Europa, amma ya sha kashi.
Ya koma Villareal, inda ya doke Arsenal a wasan kusada na ƙarshe. A wasan ƙarshe na wannan makon kuma ya doke Manchester United.
Emery