TSADAR RAYUWA: Tsawon watanni 11 farashin kayan abinci ya na hauhawa bai sauka ba – FAO

0

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta fito da sabbin alkaluman tsadar kayan abinci a duniya, wanda ya nuna zuwa watan Afrilu da ya gabata, an shafe watanni 11 a jere farashin kayan abinci na hauhawa ba tare da saukar akasarin su ba.

FAO ta bayyana cewa kayan abincin da su ka kara tsada a cikin watan Afrilu har da sukadi, man ja, man girki, nama, masara, alkama da man waken soya sauran kayan abinci da na masarufi daban-daban.

FAO wadda ke bin diddigin fasashin kayan abincin da ake hada-hadar cinikin sa a duniya, ta ce a cikin watan Afrilu kayan abinci sun yi tsadar da tun 2014 ba a samu irin tashin farashin lokaci guda ba.

“Sukari ya karu da kashi 39% tun daga watan Maris, sakamakon hauma-haumar sayen sa bagatatan da aka rika yi a duniya, saboda tsaron yankewar sa a kasuwa, saboda manyan kasashe masu sarrafa sukari irin su Brazil da Faransa ba su noma rake yadda aka yi tsammani ba a kakar 2020/2021.

Brazil kuma ta samu cikas din karyewar darajar kudi idan aka canja da dala, abin da ya shafi fitar da sukari kasashen waje da dama kamar yadda aka saba.

Sauran kayan abincin da farashin su ya kara hauhawa a watan Afrilu, sun hada da man waken soya, man ganyayyaki, man ja da kuma masara.

Kasashe da dama masu sarrafa man ja, ba su samu noma mai yawan da su ka sayar a waje sosai ba.

Yayin da farashin nama ya shi ma ya karu, haka farashin masara ya karu da kashi 5.7% a cikin watan Afrilu, 2021 kamar yadda rahoton FAO ya tabbatar.

Share.

game da Author