TASHIN HANKALI: Korona ta darkaki kasar da ta fi kowace kasa yin rigakafin Covid-19

0

Kasar Seychelles da ke Arewa maso Gabas da Madagascar, a kan Tekun Indiya, ta shiga rudani ganin yadda cutar korona da ba ta jin dafin magani sosai ta darkaki kasar, duk kuwa da cewa Seychelles din ce ta fi kowace kasa yi wa al’ummar ta alluran rigakafin korona a duniya.

Bincike ya gano yawan mutanen da aka yi wa allurar rigakafin korona a kasar kamar haka:

1 – Kashi 71% na mutanen kasar an yi masu allurar rigakafin korona ta

2 – Kashi 62% na mutanen kasar kasar an yi masu rigakafin korona ta 1 da ta 2.

3 – Kashi 57% na mutanen kasar, an yi masu allurar rigakafi ce samfurin Sinopharm Vaccine.

4 – Kashi 43% na mutanen da aka yi wa allurar, an dirka masu samfurin AstraZeneca.

Sai dai kuma duk da wannan namijin kokari da kasar ta yi, cutar korona ta kara darkakar kasar, inda kididdiga ta nuna cewa:

5 – An samu kashi 37% sabbin kamuwa da cutar korona.

6 – Kashi 20% na sabbin kamuwa da cutar korona a kasar, wadanda ke kwance a asibiti, duk sun karbi alluran rigakafin korona ta 1 da ta 2.

7 – Seychelles ta bijiro da sabbin dokoki tsaurara hanyoyin dakile cutar.

Yayin da ake kara samun masu kamuwa da cutar, masu nazari na ganin cewa akwai yiwuwar:

8 – Adadin yawan wadanda aka dirka wa allurar rigakafin ba su kai yawan adadin da za su hana cutar yaduwa a cikin kasa ba. Wato kashi 62% bai isa ya hana cutar yaduwa ba.

9 – And kasa dakile cutar saboda ba duk wadanda aka yi wa rigakafin ne aka yi wa allaran guda biyu ba.

10 – Akwai yiwuwar kangararriyar cutar korona wadda ba ta jin magani kadai, sai an yi da gaske, ta na cikin kasar ba ta fita ba.

11 – Kangararriyar cutar korona irin ta Indiya mai saurin kisa, wato B1617 ta fi saurin kamu, kuma ta fi wahalar jin magani.

Share.

game da Author