Tarin fuka na yin ajalin mutum 18 cikin awa daya a Najeriya – Kwararru

0

Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta saka cutar tarin fuka cikin shirin inshoran lafiya a kasar.

Ma’aikatan lafiya sun ce yin haka zai taimaka wajen samar da isassun kudaden da gwamnati ke bukata wajen inganta kula da masu fama da cutar ke samu a kasar nan sannan masu fama da cutar za su iya samu kula cikin sauki.

An tattauna wannan batu a taron inganta kiwon lafiya karo na hudu da aka yi a Abuja a cikin wannan mako.

Jami’in Kungiya mai zaman kanta ‘Stop TB Partnership’ Emeka Ogbuabor ya koka kan yadda rashin isassun kudade ke kawo wa yaki da cutar a kasar nan cikas.

Ya ce bincike ya nuna cewa cutar na kisan mutum 18 a cikin awa daya a kasar nan.

“Matsalar rashin isassun kudade domin yaki da tarin fuka ya kai kashi 70% a kasar nan.

“A shekarar 2019 kashi 23% na kudaden da muka kashe wajen yaki da cutar mun samo su ne daga tallafin kungiyoyin bada agaji, gwamnatin Najeriya ta samar da kashi 7% kawai.

Tarin fuka

Tarin fuka cuta ce dake kama huhu mutum inda kwayoyin cutar na Mycobacterium tuberculosis ke hadassa cutar a jikin mutum.

Sakamakon bincike ya nuna cewa Najeriya na cikin kasashe 30 da cutar ta yi wa katutu a duniya sannan na daya a jerin kasashen Afrika da suka fi samun mutanen dake da cutar ba tare da gwamnati ta san da zaman su ba.

Yin allurar rigakafi na cikin hanyoyin samar da kariya daga kamuwa da cutar amma wani sakamakon bincike da kungiyar lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa cutar na kisan mutum 245,000 sannan wasu mutum 590,000 na kamuwa da cutar a shekara a duniya.

Sannan daga cikin mutum 590,000 dake kamuwa da cutar mutum 140,000 na dauke da cutar kanjamau.

Sakamakon binciken da kungiyar ‘Stop TB Partnership’ ta gudanar a kasar nan a watan Maris ya nuna cewa an samu ragowa a yin gwajin cutar da karban maganin cutar a shekaran 2020.

Binciken ya kuma nuna cewa Najeriya ta samu koma baya a ci gaban da aka sama a yaki da cutar a wannan shekara.

Share.

game da Author