Sakamakon binciken da aka gudanar a jihar Anambra ya nuna cewa mutum daya cikin mutum 13 na dauke da cutar tarin fuka ba tare da sun sani ba a jihar Anambra.
Binciken ya kuma nuna cewa mutum 1,200 sun kamu da cutar a cikin watanni uku da suka wuce a jihar.
Shugaban shirin dakile yaduwar tarin fuka da kuturta na jihar Ugochukwu Chukwulobelu ya sanar da haka a lokacin da ya kai wa shugaban hukumar NOA Charles Nwoji ziyara a garin Awka ranar Juma’a.
Chukwulobelu ya ziyarci hukumar ne domin ya nemi goyan bayan hukumar wajen wayar da kan mutane game da tarin fuka a jihar.
Ya ce rashin sanin da rashin isassun kudade domin dakile yaduwar cutar na cikin matsalolin da shirin ke fama da su a jihar.
A dalilin haka ya sa jihar ta zama jihar da cutar ta fi yi wa katutu a kasar nan.
“Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa tarin fuka na cikin jerin cututtuka 10 dake kisan mutane a duniya.
“Binciken ya nuna cewa cutar na kisan mutum 18 a cikin awa daya a kasar nan sannan mutum 10 zuwa 15 na kamuwa da cutar a jikin mutum daya dake dauke da ita.
“Tarin fuka cuta ce da ake iya kamuwa da ita ta hanyar shakar iska amma ana iya warkewa idan aka gano cutar da wuri.
Chukwulobelu yace ya kamata a wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin da za su iya kiyayewa domin guje wa kamuwa da cutar.
Ya ce akwai asibitoci sama da 600 dake kula da masu fama da cutar kyauta a jihar.
Chukwulobelu ya yi kira ga mutane da su yi gaggawar zuwa asibiti a duk lokacin da suka ga wani ko su da kansu na da alamun cutar.
Nwoji ya yi alkawarin mara wa shirin dakile da wayar da kan mutane game da jihar a jihar Anambra.