Mai baiwa shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kana harkokin watsa labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa tabbas ƴan Najeriya za su yi matukar Kewar sa bayan ya kammala wa’adin mulkin sa wanda saura masa shekara biyu ne.
“Lokacin da gwamnatin nan ta cikashe sauran shekaru biyun da suka rage mata, babu abin da ƴan Najeriya za su rika tashi da kwana da shi suna yi mata a koda yaushe, illa tafi, jinjina da fatan alkhairi da irin nasarorin da gwamnatin ta samar wa ƴan kasa a tsawon shekarun da ta yi tana mulki”
Wa’adin mulkin shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai cika ne a 2023, a wannan lokaci zai mika mulki ga sabuwar gwamnati wanda za a zaɓa a farkon 2023.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Shugaba Buhari ya cika shekaru biyu cur yana mulkin Najeriya, wato shekara ta biyu cikin zangon sa ta biyu.
Sai dai kuma da yawa ƴan Najeriya na kuka da yadda matsaloli musamman na tsaro da ya yi tsanani a faɗin ƙasar.
Sai dai kuma akwai wasu ayyuka da gwamnatin tarayya ke alfahari da su cewa sun samu nasarar aiwatar da su a karkashin wannan gwamnati.