TABARBAREWAR TSARO: Shirun ya isa haka nan, ya kamata Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi -‘Yan Majalisa

0

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta bayyana damuwar ta, ganin duk da irin yadda matsalar tsaron kasar nan ke ci gaba da tabarbarewa, amma Buhari ya yi shiru ya ki cewa komai.

Da ya ke bayani a madadin sauran, Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Noheem Adams ya ce shirun da Shugaba Buhari ya yi ya isa haka nan. Ya kamata ya fito ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi.

Adams ya ce Majalisar Dokokin Legas na goyon bayan dukkan kudirori 12 da Gwamnonin Kudu 17 su ka bijiro da su, domin magance matsalar tsaro a kasar nan.

Ya kara da cewa tun tuni dama Majalisar Dokokin Legas na goyon bayan a bar kowace jiha ta kafa ‘yan sandan kan ta da kan ta.

Daga nan ya yi kira ga ‘Yan Majalisar Dokokin sauran jihohi su mara wa gwamnonin su baya wajen ganin an cimma cikar kudirorin da su ka bijiro da su, ciki har da kafa ‘yan sandan jihohi da sauya fasalin kasa.

To sai dai kuma ya yi kira ga gwamnonin Najeriya su fara yin tsarin sauya fasalin kasa daga jihohin su, ta hanyar bai wa Majalisar Dokoki ta Jihar ‘yancin cin gashin kai.

Ya tunatar da yadda Kakakin Majalisar Jihar Legas, Mudashir Obasa a matsayin sa na Shugaban Majalisar Kakakin Majalisun Dokokin Najeriya ya ja tawagar su zuwa Fadar Shugaban Kasa, inda su ka nemi ya sa wa dokar cin gashin kan Majalisar Dokokin Jihohi hannu.

Ya ce tun tuni ya kamata a sauya fasalin Najeriya, ta yadda zamantakewa da juna a tsakanin bangarori za ta fi kasa danko sosai.

Share.

game da Author