TABARBAREWAR TSARO: Gwamnonin APC bakwai sun watsa wa Buhari kasa a ido

0

Gwamnonin APC bakwai na daga cikin gwamnoni 17 na kudancin Najeriya, wadanda su ka nuna wa Shugaba Muhammadu Buhari tantagaryar gazawar wa wajen shawo kan matsalar tsaro a fadin kasar nan, a ranar Talata.

Gwamnoni 15 tare da wakilcin mataimakan gwamnoni biyu ne su ka yi taro a Asaba, babban birnin Jihar Delta, inda a ranar Talata su ka fito wa Shugaba Buhari da kudirori 12 domin magance tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Gwamnonin APC da su ka halarci taron na Asaba sun hada da Sanwo Olu na Lagos, Gboyega Oyetola na Osun, Dapo Abiodun na Ogun, Kayode Fayemi na Ekiti, Hope Uzodinma na Imo, Dave Umahi na Ebonyi da Rotimi Akeredolu na Ondo.

Akwai Gwamnonin PDP tara sai kuma Gwamna Willie Obiano na Anambra daga jam’iyyar APGA.

Abin mamaki ma shi ne yadda dukkan gwamnonin APC ba su nuna ja-in-ja a kan batutuwan da aka tauna ba.

Sannan kuma Gwamnan APC ne, Rotimi Akeredolu na na Ondo ya shugabanci taron. Kuma shi ne ya yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron.

Jama’a da dama na ganin cewa kudirorin da gwamnonin kudu 17 su ka zartas, sun yi kamanceceniya da wasu kudirori da gwamnonin APC su ka taba zartaswa a wani taron su cikin 2018.

Ana ganin mai yiwuwa gwamnatin tarayya ta dauki batun na gwamnonin kudu da muhimmanci, har ta tashi tsaye ta yi rawar gani wajen gaggauta shawo kan matsalar tsaro.

Muhimman Bukatun Da Gwamnonin Kudu 17 Ke Nema Kan Matsalar Tsaro, Rashin Adalci A Raba Manyan Mukamai, Fulani Makiyaya Da Sake Fasalin Rabon Arzikin Kasa.

1. Mu Gwamnonin Kudu 17 mu na kara jaddada bukatar ganin cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya, amma a bisa turbar adalci ga kowane bangare na yankin kasar nan baki daya.

2. Mun lura cewa kwararar makiyaya masu dauke da muggan makamai da sauran manyan masu laifuka zuwa cikin yankin Kudanci, lamarin na kara nuna irin matsalar tsaron da ta kai jama’a su na zaune cikin halin kasa gudanar da rayuwar su da ta hada da kasuwanci da harkokin noma da bunkasa tattalin arziki. Wannan kuwa ya haifar da barazana ga samar da abinci da kuma barazana ga tsaro baki daya.

To dalilin haka mun hana kiwo kwata-kwata a jihohin kudu. Wato kiwon da ba a iya daure dabbobi a ciyar da su, sai dai a rika gararambar yawo da su ana neman abinci.

3. Mun hana yawon kiwo ana karkado dabbibi daga Arewacin kasar nan ana nauso mana da su nan Kudu.

4. Mun goyi bayan Gwamnatin Tarayya cewa ta fito ta taimaka wa duk jihar da ta ga za ta yi tsarin kiwon dabbobi na zamani.

Don haka mu na bukatar a gaggauta sauya fasalin Najeriya ta yadda za a amince kowace jiha ta kafa ‘yan sanda na kan ta. Kuma a sake fasalin rabon arzikin kasa, a sake fasalin rabon kudaden shiga ta yadda tsarin zai fifita jihohin da aka fi samo arzikin daga yankunan su. Wannan shi ne zaman gaskiya, babu cuta ba cutarwa na tsarin federaliyya ta zahiri.

5. Mu na sanar da cewa saboda masu tayar da jijiyoyin wuya a kasan, mu na kira da a gaggauta kiran taro na kasa.

6 Akwai bukatar a sake duba irin yadda aka yi nade-naden mukamai yanzu haka a Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Tarayya, ciki kuwa har da Hukumomin Gwamnati.

7. Mu Gwamnonin Kudancin Najeriya na kira ga gaggawa a kira Babban Taron Tattaunawa na Kasa, ganin yadda bangarorin kasar nan ke ta karajin korafe-korafen neman a rika tafiya tare da kowane sashi a tafiyar da gwamnati.

8. Mun zartas cewa akwai bukatar mu kara dankon zumunci da hadin kai tsakanin Jihohin Kudu da kasar nan baki daya.

9. Mun matukar damu da yadda ake samun matsanancin cinkoson motoci a kan babban titin Apapa, tashar ruwan da can ne jijiyar tattalin arzikin Najeriya. Wannan cinkoso na kawo koma baya sosai ga tattalin arziki.

Saboda haka mun zartas da cewa Gwamnatin Tarayya ta gina karin tashoshin jirage a wasu jihohi domin saukake wancan cinkoso na Tashar Apapa.

10. Mun damu da kokarin sake kulle kasar nan saboda korona. Saboda kullewar za ta haifar da matsananciyar matsalar tattalin arziki. Saboda haka mu na kira Gwamnatin Tarayya ta hada karfi da Gwamnatocin Jihohi domin a bijiro da hanyar dakile cutar korona ta bai-daya.

11. Mu na matukar damuwa da gagarimar matsalar tsaro da ke ci gaba da dagulewa a kasar nan. Ya kamata Shugaban Kasa ya yi wa jama’ar kasar nan jawabin da zai kara wa mutanen kasar nan kwarin guiwa.

12. Mu na matukar godiya ga Gwamna Ifeanyi Okowa saboda daukar nauyin wannan taro da ya yi da kuma karimcin da ya nuna mana yayin taron.

Share.

game da Author