“Lamari ya tabarbare, rashin tsaro ya yi munin da babu sauran wurin tsiya. Ba ganakin ba, ba kasuwannin ba. Ba makarantun ba, ba cikin gidajen ba. Ba a masallatan ba, ba a coci-coci ba. Ba a yankunan karkara ba, ba a cikin birane ba. Ko’ina daga zaman dardar sai tashe-tashen hankula. Babu sauran wurin gudu a buya ko a tsira.”
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta dawo da sojojin da su ka yi ritaya domin su taimaka wajen yakar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.
Abubakar ya yi wannan bayani cikin wata takarda da ya fitar a ranar Talata, dangane da yadda tsaro ke kara tabarbarewa a kullum a kasar nan.
Atiku ya nuna fargabar cewa wannan matsala a kullum sai kara gaba ta ke yi, amma gwamnati ta kasa dakile ta.
“Lamari ya tabarbare, rashin tsaro ya yi munin da babu sauran wurin tsiya. Ba gonakin ba, ba kasuwannin ba. Ba makarantun ba, ba cikin gidajen ba. Ba a masallatan ba, ba a coci-coci ba. Ba a yankunan karkara ba, ba a cikin birane ba. Ko’ina daga zaman dardar sai tashe-tashen hankula. Babu sauran wurin gudu a buya ko a tsira.
“‘Yan ta’adda sai kara darkakowa da nausawa sassan kasar nan su ke yi, daga Arewa maso Gabas har sun kai Arewa ta Tsakiya, cikin Jihar Neja. Kenan kadan za su kara tafiyar ‘yan sa’o’i kadan su danna cikin Abuja, babban birnin tarayya.
“Saboda haka ina yin kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kiran sojojin da su ka yi ritaya, mazan su da matan su, domin su dawo su taimaka wajen yaki da ‘yan ta’adda har sai an kakkabe su baki daya, an murkushe su.”
Atiku ya yi wannan kira ne bayan Gwamnan Jigawa da na Bauchi sun yi kururuwar bullar Boko Haram a jihohin su.
Haka kuma idan ba a manta ba, shi ma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya shawarci Shugaba Buhari cewa, “tunda matsalar tsaro ta fi karfin Shugaba Buhari, to ya gaggauta neman taimako ko ma daga wace kasa ce, domin a taru a yi wa matsalar tsaro kwaf-daya.
Discussion about this post