Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai yin biyayya da da’a ga iyaye, a lokacin da suke raye da kuma bayan mutuwarsu, yana daga cikin manyan farillai da wajibai da Allah ya rataya a kan kowane Musulmi, in dai har Musulmin kwarai ne. Kai yana ma daga cikin mafiya girman ayyukan Ibadah, bayan bautar Allah Ta’ala. Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:
“Ku bauta wa Allah, kada ku yi masa shirka da komai. Kuma ga iyaye ku kyautata.” [Suratun Nisa’i: 37]
Sannan wata rana an tambayi Manzon Allah (SAW) game da mafiya soyuwar ayukka a wurin Allah, sai ya amsa da cewa:
“Yin Sallah a kan lokacinta. Aka ce sai me? Yace: “Yin biyayya da da’a ga iyaye.” Aka ce sai wane? Yace: “Yin Jihadi a kan tafarkin Allah (wato jihadi na gaskiya, ba irin na ‘yan ta’adda ba).” [Buhari da Muslim]
Kuma Allah Madaukakin Sarki yace:
“Kuma mun yi wasiyyah ga mutum game da iyayensa, mahaifiyarsa ta dauke shi wahala kan wahala ta kuma shayar da shi na shekara biyu, (don haka) ka gode mani kuma ka gode wa iyayenka, (sannan) gare ni makoma take.” [Suratu Lukman: 14]
Da kuma inda Allah yayi umarnin a kyautata masu, musamman idan sun tsufa, yace:
“Ubangijinka Ya hukunta cewa kada ku bauta wa kowa face Shi. Kuma game da iyaye ku kyautata masu, koda dayansu ya tsufa ko dukkansu biyu, kada kace masu tir! Kuma kada kayi masu tsawa (ko ka kwance masu zani a kasuwa), ka gaya masu magana mai dadi. Ka tausasa masu fika-fikan rahama kuma kace: “Ya Ubangiji Kayi masu rahama, Ka tausaya masu, kamar yadda suka rene ni ina karami.” [Isra’i: 23-24]
Kuma Annabi Muhammad (SAW) yayi Allah waddai da wanda bai yi wa iyayensa biyayya da da’ar da zasu kai shi Aljannah ba, yayi addu’a, yace:
“Ya Allah ka turmusa hancinsa, ya Allah ka turmusa hancinsa, ya Allah ka turmusa hancinsa!” Sai Sahabbai suka ce wanene ya Manzon Allah?” Sai yace: “Wanda ya riski mahaifansa lokacin tsufansu, ko daya daga cikinsu ko dukkansu biyu, amma bai shiga Aljannah ba.” [Muslim]
Annabi (SAW) ya nuna cewa rashin da’a da biyayya ga iyaye yana daga cikin manyan zunubai, in da a wani wurin Annabi (SAW) ya nuna cewa, a cikin manyan zunubai, daga shirka sai sabawa iyaye. Wannan yana nuna bayan hakkin Allah sai hakkin iyaye kenan.
Don haka mu sani, kyautata wa iyaye, da da’a da biyayya gare su dole ne, tilas ne, kuma wajibi ne, kuma wannan har bayan ransu, kai ko da ace kafirai ne, wajibi ne ayi masu biyayya a cikin komai da komai, in dai ba sabon Allah da Manzonsa ba ne.
Wajibi ne, kuma wallahi dole ne, duk wani mataki da iyaye suka dauka, ko wani hukunci da suka zartar lokacin rayuwarsu, a tabbatar da shi, ko da bayan ransu ne! Don haka, kar wani da daga cikin ‘ya ‘ya, ya zama dan kuka, ya tayar da wani hukunci, ko wani mataki, da mahaifinsa ya dauka, don kawai yana ganin yanzu baya raye, ko kuma don wani ya tursasa masa yin hakan, ko kuma don kwadayin abun duniya, ko kuma don yana so ya faranta ran wani mutum. Duk kuwa wani da da yayi haka, to ya sani, wallahi, wallahi, wallahi, shi ba dan kwarai bane, ba dan kirki bane, ba dan goyo bane, kuma ba dan arziki ba ne. Domin yin haka yana nuna cewa, YA KWARE WA MAHAIFINSA ZANI NE A KASUWA! Kuma wallahi shima sai Allah ya tayar da wadanda za su yi masa haka, domin a ramawa mahaifin nasa abunda yayi masa na cin mutunci!
Jama’ah wajibi ne a dadada wa iyaye, dole ne a kyautata masu, kuma a kyautatawa duk wanda suke so a kyautata masa, dole ne ayi duk abunda za ya sa suji dadi, su samu natsuwa da farin ciki, a lokacin rayuwarsu da kuma bayan ransu, matukar abin nan ba sabon Allah ba ne da Manzonsa (SAW). Abdullahi (RA) yace:
“Na tambayi Manzon Allah (SAW) cewa wane aiki ne Allah mai girma da daukaka yafi so sai yace: “Sallah akan lokacinta, sai nace sannan wane? Sai yace: Bin Iyaye, sai nace sannan wane? Sai yace: Sannan Jihadi don daukaka kalmar Allah. Sannan yace Annabi (SAW) ne ya fada man wadannan abubuwa muhimmai, kuma da naso ya kara man da ya kara man.”
Abdullahi dan Umar (RA) yace:
“Yardar Allah tana cikin yardar iyaye, kuma fushin Allah yana cikin fushin iyaye.”
Wato wanda iyayensa suka yarda da shi, to Allah za ya yarda da shi, haka ma idan iyayensa suna fushi da shi, to Allah ma yana fushi dashi. A wani hadisin kuma Abdullahi dan Abbas yace:
“Lallai ni ban san wani aiki wanda yafi kusanci zuwa ga Allah ba fiye da biyayya da da’a ga iyaye.” [Duka Hadisan suna cikin Al-Adabul Mufrad, na Imamul Bukhari]
Don haka mu sani, duk mutumin da ya warware wani hukunci, ko wani mataki da mahaifinsa ya dauka, a lokacin da yake raye, wannan mutum ya sani, wallahi yaci amanar mahaifinsa, yaci mutuncinsa, kuma wallahi yayi masa babban butulci, kuma sai Allah ya kama shi akan wannan mummunan aiki da yayi, kuma wannan mutum, da ikon Allah, ba zai taba cin nasara ba a rayuwarsa!
A yau wannan zamani, jama’ah, an wayi gari, wasu daga cikin ‘ya ‘yan wannan zamani, marasa mutunci, suna rungumar makiyan iyayensu a matsayin masoya, ainihin masoyan iyayensu na gaskiya kuwa, sai su dauke su sune makiyansu! Wal iyazu Billah! Wace irin rayuwa ce wannan muke cikin ta don Allah? Yanzu masu yin irin wannan, don Allah suna tsammanin iyayensu zasu samu natsuwa da su, a cikin kabarinsu?
Lallai masu aikata irin wannan ta’asa, su kwana da sanin cewa, yanzu haka, iyayensu suna can cikin kabari, suna tsine masu albarka, kuma suna yin Allah waddai da mummunan aikin da suka yi.
Idan ba dolonci, da wawanci, da miskilanci ba, don Allah ta yaya mutum zai kwancewa ubansa zani a kasuwa, ta hanyar rungumar wadanda suka yi mummunan fada da mummunar adawa da mahaifinsa? Mutanen da duk duniya ta shaida cewa, su ba masoyan ubanka bane; sun zage shi, sun ci zarafinsa, sun bata masa rai, sun nemi su walakanta shi, amma Allah ya kare shi, wai ace wadannan mutane, a yau, sune mutanen ka, da kake mu’amala da su? Wai domin Allah, kai wane irin da ne a wurin wannan mahaifi naka mai daraja?
Mahaifanka da magabatanka sun haife ka, sun yi tarbiyyarka har ka zama mutum, kuma suna zato da tsammanin cewa, zaka kare mutuncinsu da martabarsu, a lokacin rayuwarsu da kuma bayan mutuwarsu, amma ace wai kai ne, za’a hada kai da kai, aci mutuncinsu, a kwance masu zani a kasuwa, a wulakantasu, a mayar da su ba bakin komai ba, saboda ganin basa raye, kuma kayi tsammanin zaka zauna lafiya, zaka gama lafiya, zaka wanye lafiya! Wallahi ba zai taba yiyuwa ba!!
Daga karshe, Manzon Allah (SAW) yace:
“Yana daga cikin cikar biyayya da da’a ga iyaye, mutum ya sadar da zumuncin da ke tsakanin abokai da masoyan mahaifansa.” [Muslim]
Ya Allah, muna rokon ka shiryar da mu tafarki madaidaici, ka nuna muna gaskiya, ka bamu ikon bin ta, ka nuna muna karya, ka bamu ikon guje mata. Ya Allah, ka bamu ikon yin adalci da fadar gaskiya akan ko waye, amin.
Wassalamu alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.