Rundunar Sojojin Najeriya ta sauya sunan Yakin Boko Haram daga ‘Operarion Lafiya Dole’ zuwa ‘Operarion Hadin Kai’.
Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya Mohammed Yerima, ya fitar da sanarwar cewa an sauya sunan saboda irin gagarimar nasaarar da aka samu.
“Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya amince da sauya sunan shirin yaki da Boko Haram, daga ‘Operation Lafiya Dole (OPLD) zuwa ‘Operation Hadin Kai (OPHK’).”
Attahiru ya ce an canja sunan salon yakin ne saboda a baya an samu gagarimar nasara a kan Boko Haram.
“Janar Attahiru ya hakkake cewa samun nasarar yaki da Boko Haram har a kawar da su kwata-kwata, abu ne da ke matukar bukatar dukkan daukacin ‘yan Najeriya.”
Ya kara alwashin cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da matsa lambar ganin sun kakkabe sauran burbushin Boko Haram baki daya a kasar nan.
Cikin 2015 ne Janar Tukur Buratai bayan ya zama Babban Hafsan Sojojin Najajerya, ya canja sunan Yakin Boko Haram daga ‘Operation Zaman Lafiya’ zuwa ‘Operation Lafiya Dole’.
A wancan lokacin Buratai ya ce ya canja sunan saboda za a kama yaki ne gabagadi, ba wai cacar baki ba.
Sai dai duk da sauye-sauyen da ake wa sunan yaki da Boko Haram, har yau ana ta gaganiyar neman kakkabe su, amma abin ya faskara.
Discussion about this post