Shugaban Kotun CCT, ya bayyana gaban Majalisar Dattawa, bayan maigadin da ya kifa wa mari ya kai mata karar sa

0

Shugaban Kotun CCT, Danladi Umar ya bayyana a gaban Kwamitin Sauraren Korafe-korafe a ranar Talata, a Majalisar Dattawa.

Bayyanar ta sa ta biyo bayan karar sa da mai gadi a Rukunin Kantinan Hada-hadar Kasuwanci na Banex Plaza da ke Wuse, Abuja, mai suna Clement Sagwak ya kai karar sa biyo bayan kifa masa mari da shugaban na CCT ya rika yi a harabar plaza din da ya ke gadi.

Sagwak ya rubuta wa Majalisar Dattawa korafin cin zarafi da cin fuska da tozartawar da Danladi ya yi masa a gaban jama’a kwanakin baya.

Wasikar dai Sagwak ya rubuta ta ne ta hannun lauyan sa mai suna Timzing Ramnap, kuma Sanata Istifanus Gyang na Shiyyar Filato ta Arewa ne ya yi wa takardar korafin jagora a gaban Majalisar Dattawa, a ranar 29 Ga Afrilu.

An gayyaci Umar aka ce ya bayyana domin ya kare kan sa.

Sai dai kuma a lokacin da Umar ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya, ya ce ba a aika masa da kwafen na korafin da ake yi a kan sa ba.

Daga nan sai ya bukaci a ba shi kwanaki bakwai domin ya je ya zauna ya yi nazarin korafin da ake yi a kan sa, ta yadda zai amsa batutuwan kamar yadda ya dace.

Daga nan dai an ba shi makonni biyu domin zuwa ya yi nazarin korafe-korafen da mai gadin ya yi a kan sa na zargin dukan da ya ce mai shari’a Umar ya yi masa.

Shugaban Kwamiti Ayo Akinyelure ne ya ce ya bai wa Umar har makonni biyu domin zuwa ya samu lokacin yin nazarin korafin, wato daga nan zuwa ranar 18 Ga Mayu.

Ya ce duk da Majalisa za ta tafi hutun makonni biyu daga ranar Alhamis, duk da haka kwamitin zai dawo a cikin hutun domin ya yi zaman sauraren ba’asin Shugaban Kotun CCT din.

Share.

game da Author