Shekau ya yi kukan kura ya kashe kansa da gaggan ‘ yan Boko Haram bangaren ISWAP

0

Akalla sau hudu ana sanar da mutuwan Abubakar Shekau a baya amma kuma sai ya bayyana a bidiyo yana cewa bai mutu ba.

Wannan karon jaridar HumanAngle ta ruwaito cewa lallai Shekau ya kashe kansa a wani arangama da suka yi da kungiyar Boko Haram bangaren ISWAP.

Jaridar ta ruwaito cewa ISWAP sun yi batakashi da Boko Haram bangaren Shekau, amma kuma Shekau da makarraban sa basu yi nasara ba.

Bayan sun fi karfin Shekau da mayakan sa sai suka tilasta shi yayi mubaya’a, wato ya bada hadinkai, ya mika wuya ga ISWAP.

Shekau daure a jikinsa ashe bamabamai ne, sai da ya natsu cikin shugabannin ISWAP a daidai sun bashi zabin ko ya mika wuya ko ya kwan ciki sai ya tada bamabaman dake daure a jikin sa gaba dayan su suka mutu tare da shi.

Saidai jaridar bata fadu ko suwaye cikin shugabannin Boko Haram na bangaren ISWAP suka mutu ba.

Ba tun yanzu ba ak samu baraka a bangaren Boko Haram dake karkashin Ikon Shekau ba. Tun bayan rarrabuwa da aka samu, inda wasu suka koma bangaren Boko Haram na ISWAP, suka fara kaiwa juna hare-hare.

Rikici kan auku ne idan bangaren Shekau suka afka yankin bangare ISWAP, suka yi musu sata ko kuma kwashe musu mata da abinci.

Daga baya sai su kawo musu harin daukan fansa.

Yanzu dai an samu wawukeken baraka a tsakanin bangarorin Boko Haram dake zaune a iyakokin Najeriya, Nijar da Chadi.

Share.

game da Author