Sheikh Mahi Niass ya tabbatar wa Sanusi Lamido, Khalifancin darikar Tijjani a Najeriya

0

Sugaban darikar Tijjaniya duniya, sheikh Mahi Niass, ya tabbatar wa sarki Sanusi II khalifancin darikar Tijjaniya na Najeriya baki daya.

Sheikh Niass ya gayyaci Sarki Sanusi shan ruwa a garin Kaolack, kasar Senegal, in da a nan ne ya jaddawa sarki Sanusi wannan shugabancin da aka yi masa na jagorar darikar Tijjaniya a Najeriya.

Idan ba a manta ba, wakilin Sheikh Niass, ya sanar da nadin Sarki Sanusi sabon Khalifan Tijjaniya a Najeriya wanda ya gaji marigayi, Isiyaka Rabiu a garin Sokoton Najeriya a taron Maulidi da darikar ta yi.

Sai dai bayan wannan taro, ‘yan bangaren sheikh Dahiru Bauchi, suka ki amincewa da wannan nadi, inda daya daga cikin’ ya’yan sa Ibrahim Nahiru Bauchi, ya karyata nadin yana mai cewa, ba a yi haka ba.

Niass ya hori sabon Khalifan ya rike mutane da adalci kamar yadda yake a addinin musulunci.

Share.

game da Author