Saƙon Sallah daga Sanata Bola Ahmed Tinubu (Jagaban Borgu)

0

Mu yi riƙo da darussan da  mu ka koya a Ramadan

A yau rana ce ta farin ciki da muka sauke daya daga cikin ginshikan addini da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya ɗora mana, wato azumin watan Ramadan wanda  ɗaya ne daga cikin shika shikan musulunci guda biyar masu muhimmanci.

A matsayinmu  na Musulmi mun shafe wata guda muna azumi da ibadu na musamman duk domin neman dacewa da samun falalar Ubangiji. Musulmi sun sadaukar da kai, ta hanyar jurewa yunwa da ƙishirwa da dukkanin wasu abubuwa na jin daɗin rayuwa da Allah ya hana, tun daga ketowar alfijir har zuwa almuru. To amma ina ganin akwai hikimar Allah a cikin wannan umarni na Allah (SWT) da ya bayar ga muminai, bawai kawai ya umarce mu mu yi azumi bane a matsayin ibada kawai, ko don mu nunawa duniya mu na daban ne, ko shakka babu akwai darussa na rayuwa baya ga ibada a maganar azumi.
 
Tabbas mun juyawa  ababen jin dadin rayuwa na yau da kullum baya kamar yadda Allah ya hore mu, domin mu ƙara jaddada imanin mu, mu koyi haƙuri, juriya, ƙarfin hali da kuma ƙaunar juna. Wannan shi ne maƙasudin yin azumi, domin a koda yaushe mu ƙara ƙarfin imanin mu, mu kuma riƙe waɗancan darussa na rayuwa. Haka kuma azumi wata dama ce da mu ke samu domin mu ƙara samun kusanci da mahaliccinmu,  mu kuma zama masu godiya saboda irin ɗimbin rahamar sa a gare mu. Saboda haka,  babban abinda azumi ya koyar shi ne soyayya, ƙauna, tausayi, da  mutunta juna. Babban abinda Ramadan ke koyarwa shi ne, mutunta juna da nuna ƙauna ga kowa da kowa, ba tare da nuna bambanci ba.
 
A wannan lokaci da wannan wata mai albarka ke ƙarewa, lokaci ya yi da kowa zai zauna ya yi nazari kan yadda za mu ci moriyar waɗannan darussa bayan wucewar Ramadan. Ya zama wajibi mu zama wannan ibada ta sanya mana ƙauna da son juna a tsakaninmu. Ya zama wajibi mu gina al’umma ta gari, wacce kowa zai alfahari da ita ba tare da wani tashin hankali, ko ƙuncin rayuwa ba. Ya zama wajibi mu toshe duk wata kafa da za ta bawa masu son kawo tashin hankali a tsakanin mu damar aiwatar da mummunar manufar su a kan mu ta gwara kawunan mu da kawo tashin hankali.
 
Ya kamata a ce wadannan darussa na Ramadan sun zamar mana fitillar da zamu haska gwadaben da muke tafiya a kan sa. Ina kira ga yan Nijeriya da mu ajiye bambancin siyasa, mu yi amfani da wannan lokaci  mu yi wa ƙasar mu addu’ar  samun zaman lafiya. Kada m
mu manta mu sanya Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa acikin addu’ar mu, mu roƙa musu Allah ya basu karfin guiwar da za su shawo kan matsalolin da ke addabar ƙasar nan, kuma ya basu hikimar da za su ɗora  Najeriya a kan tafarki madaidaici da cigaba.
 
Ina kuma barar mu yi wa sojojin mu da jami’an tsaron mu adduar Allah ya basu nasara, ya ɗora su akan maƙiyan ƙasarmu, ya kuma ba su ƙarfin guiwar daƙile duk wata barazanar da yan ta’adda ke yi wa kasar nan. Kar kuma mu manta da waɗanda wannan ibtila’i ya shafa, musamman waɗanda suka rasa rayukan su, da waɗanda suka yi asarar dukiya da kuma waɗanda suka rasa wasu nasu, walau ƴaƴa, ko mata, ko iyaye ko kuma mazajen su, wannan kuwa ya haɗa har da waɗanda annobar  COVID-19 ta shafa.
 
Ya zama wajibi baya ga addu’a da ibada mu kuma tashi tsaye mu yi aiki tuƙuru wajen ganin mun samar da ƙasa tagari mai ɗorewa. Kowannen mu makiyaya ne, kuma kowa za a tambaye shi akan abinda aka ba shi kiwon kamar yadda hadisin Annabin Muhammad (SAW) ya bayyana.
 
Muna addu’ar Allah yadda wannan wata ya zo karshe,  ka karɓi ibadun mu, ka sanya mu cikin bayinka yantattu, ka yafe mana kura-kuran mu, ka baiwa ƙasarmu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali. Allah ya bamu damina mai albarka.
Barka da Sallar Eid-el-fitri!
 
Sahannu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
May 12, 2021.

Share.

game da Author