Rundunar Sojin Najeriya ta kama wasu da ake zaton ‘ yan Boko Haram ne su 13 a Unguwar Filin Lazio, a Hotoro dake jihar Kano.
Rundunar ta yi kira ga mutanen unguwar su cigaba da gudanar da al’amurorin su, cewa rundunar na bibiyar duka abubuwan dake faruwa.
” Abinda muke kira da rokon mutane akai shine su sa ido sosai, duk inda suka wulkawar wani da badu amince da shi ba su gaggauta sanar da jami’an tsaro.
Idan ba a manta ba, a cikin watan Afrilu, gwamnan jihar Neja ya bayyana cewa Boko Haram sun kwace ikon kananan hukumomi biyu a fadin jihar.
Ya zargi fadar shugaban kasa da rashin daukar kwararan mataki akai wanda ya ce daga yanzu abinda ya dace zai yi ba zai ci gaba da sauraren gwamnatin tarayya ba.
Haka shima gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya gargadi mutanen jihar su sa ido domin an samu rahoton kwararowar Boko Haram zuwa wasu yankunan jihar daga jihar Bauchi.