RUFE ƘOFA DA BARAWO: Gwamnan Neja ya lula ƙasar waje, sa’o’i kaɗan bayan sace ɗaliban Islamiyya a Tegina

0

Gwamnan Jihar Neja ya lula ƙasar waje, lokaci kaɗan bayan kwashe ɗaliban Islamiyya a ‘yan bindiga su ka yi, a Tegina, cikin Ƙaramar Hukumar Rafi.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan, Mary Noel-Berge ta ce ya tafi laluben hanyoyin da zai ƙarfafa tsaron jihar ne. Sannan kuma ta ce ya tafi ne tun kafin a sace yaran.

Ta ce Gwamnan ya tabbatar wa iyayen yara cewa ana nan ana ƙoƙarin ganin an ƙwato ko an ceto yaran na Tanko Saliu Islamiyya da aka sace a garin Tegina, bayan ‘yan bindiga sun mamaye garin kuma sun ƙwace ofishin ‘yan sandan garin na Tegina.

Gwamna Abubakar Bello ya ce ya umarci jami’an tsaro su tabbatar cewa sun ceto yaran cikin ƙanƙanen lokaci.

Sanarwar ta ce ya fita ne domin laluben yadda za a inganta tsaro a jihar Neja, wadda ‘yan bindiga da Boko Haram su ka samu gindin zama a ciki, kamar yadda Gwmnan da kan sa ya taba furtawa.

Mary ta ce ba daɗewa Gwamna Abubakar Bello zai yi ba, da ya kammala sha’anin da ya kai shi, zai koma gida Jihar Neja.

Wannan ne karo na biyu da aka sace ‘yan makaranta a Ƙaramar Hukumar Rafi, a cikin 2021. Domin a can ne aka sace ɗaliban sakandare na Kagara, a farkon wannan shekara.

PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito Gwamna Abubakar Bello na cewa halin da Jihar Neja ke ciki daidai ya ke da zamanin yaƙin ‘ƙatilan-maƙatulan’.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello ya bayyana cewa halin da Jihar Neja ke ciki ya yi munin da babu wani bambanci da zamanin yaƙin ‘ƙatilan maƙatulan’, ya ce ya kamata a san cewa yaƙi fa ake yi a Neja.

Bello ya nuna bacin ran sa ne domin ƙara sanar da halin kashe-kashe da hare-haren da ‘yan bindiga ke yi a Neja, tare kuma da sake yin kira ga Gwamnatin Tarayya domin ta kai wa Jihar Neja ɗaukin gaggawa.

Bello ya yi maganar ce ganin yadda hare-hare su ka yi yawa a Ƙananan Hukumomin Rafi, Wushishi da Lavun. Ya ce an kai munanan hare-haren a garuruwan Wushishi, Tegina da Batati.

“Lamarin fa ya yi muni fiye da yadda duk ake tsammani. Maganar gaskiya mun afka zamanin yaƙe-yaƙe. Kuma kamata ya yi a tunkari matsalar nan gadan-adan ba tare da bata lokaci ba.”

Haka Kakakin Gwamnan, Mady Noel-Berje ta bayyana cewa Gwamna Abubakar ya faɗa, cikin wata sanarwa da ta sa wa hannu a madadin gwamnan.

Ya ce za a fara bi gida-gida domin a tabbatar da yawan yara ƙananan da aka sace, aka yi garkuwa da su.

Jami’in gwamnati ya ce ‘yan bindiga kamar su 70 ne su ka karaɗe ƙauyuka 17, a cikin ƙaramar hukumar Wushishi, inda su ka harbi mutane da dama.

An kuma tabbatar da cewa ruwa ya tafi da mata da ƙananan yara, a lokacin da su ka tinjima cikin Kogin Kaduna, domin su tsira daga ‘yan bindiga.

Mutanen da ake nema ba a san inda su ke ba a halin yanzu, ‘yan garuruwan Babako ne da Tashan Jirgi, Kwakwagi,Fakars, Ndiga, Buzu, Akare, Kala Kala, Agwa, Anguwan Gizo, Tsamiya da sauran ƙauyukan da ke maƙautaka da su.” Inji Noel-Berje.

Share.

game da Author