RASHIN TSARO: Barazanar jefa wa Buhari kuri’ar-yankan-kauna ta janyo sanatocin APC da PDP sun fara kyarta wa juna ashana

0

Sanatocin Najeriya sun bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da lusaranci ko kokarin da Shugaba Muhamammadu ke yi wajen dakile matsalar tsaro a kasar nan.

Yayin da sanatocin PDP su ka yi fata-fata da Shugaba Buhari dangane shiru da bakam din da ya ke yi zaune turus a fadar sa, alhali ko’ina a kasar nan na fama da tashe-tashen hankula da kashe-kashe, su kuwa na APC cewa su ka yi Buhari na bakin kokarin sa wajen shawo kan matsalar tsaro.

Gungun Sanatoci marasa rinjaye a karkashin shugaban su, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya zargi Buhari karya dokar kasa da kuma bijre wa bakin aikin da dokar kasa ta wajibta masa, a daidai lokacin da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke ta kashe na kashewa, su sace na sacewa.

Sun kuma yi tir da tsarin tattalin arzikin Gwamnatin Buhari, saboda ya jefa kasar nan cikin kuncin rayuwa, tsadar kayan abinci, karyewar darajar naira, karin kudin fetur, karin kudin lantarki da kuma tulin haraji na babu gaira babu dalili.”

Yayin da Abaribe ke wa manema labarai jawabi a ranar Laraba, ya ce “sanatocin bangaren adawa za su yi dukkan abin da doka ta tanadar domin ceto kasar nan daga tarwatsewa.”

Dama kuma kafin nan, ‘yan Najeriya da dama sun nemi Shugaba Buhari ya sauka haka nan, tunda ya kasa magance matsalar tsaro.

To amma ba a sani ba ko batun tsigewa Sanata Abaribe ke nufi yayin da ya ce za su yi abin da dokar kasa ta amince su yi kan Buhari, domin su ceto kasar nan daga durkushewa ko tarwatsewa.

Abaribe ya yi ikirarin cewa rayuwar sanatocin da ke bayyana ra’ayin su na cikin hatsari saboda sun yi kumumuwar fada wa gwamnatin tarayya gaskiya mai daci.

“Sanatocin Bangaren Marasa Rinjaye sun tuna da farkon alkawarin gwamnatin APC tun ma kafin a yi zaben 2015 da kuma bayan zaben, shi ne alkawarin farko na samar da tsaro a kasar nan.

“Amma abin takaici daga 2015 zuwa yau, maimakon gwamnatin APC ta dakile matsalar tsaro, sai ma ta kara fadada matsalar zuwa sauran sassan kasar nan daga Arewa maso Gabas zuwa kowace shiyya ta Najeriya.

Sai dai kuma Shugaban Masu Rinjaye Sanata Abdullahi Yahaya, ya bayyana kalaman Sanata Abadibe da cewa akwai karin gishiri saboda bambancin siyasa.

Daga nan ya ci gaba da bayyana irin kokarin da Gwamnatin Buhari ke yi shi da Shugabannin Tsaro dare da rana, domin shawo kan lamarin.

Ya ce duk lokacin da wani abu ya faru, Shugaba Buhari ya na fitar da sanarwa. Sannan kuma ya dora laifin a kan Gwamnatin PDP wadda ya ce ta shafe shekaru 16 kan mulki, amma ba ta karfafa fannin tsaro a kasar nan ba.

Share.

game da Author