PDP tsohuwar rijiya ce da ‘Yan Majalisar APC ke tsoron shiga ciki – Hon. Ado Doguwa

0

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Alasan Ado-Doguwa ya bayyana cewa jam’iyyar PDP jirgin ruwan da ya kusa nutsewa a cikin teku ne, don haka babu wani Dan Majalisar Tarayya daga APC da zai yi gangancin shiga jirgin har ya nutse da shi.

Doguwa mai wakiltar Kananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa na Jihar Kano, ya bayyana haka a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa ‘yan jarida a Kano.

“Ina so na maida martani dangane da wata tatsuniya da Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Tarayya, Ndidi Elumelu ya yi, wai wasu mambobi ‘yan APC sun same shi sun yi masa kukan su na so su koma PDP, jam’iyyar da ke tangal-tangal ta na neman nutsewa a cikin teku.

Martani na a nan da kam ban yi niyyar cewa komai ba. To amma akwai batun a wanke zukatan jama’a masu tunani ko kokwanton shin wadanne mambobi din APC ne ke kokarin komawa a wannan tatsuniya ta Elumelu, shi ya na ga akwai bukatar na yi magana.

“Na san dai akwai taron da shugabannin majalisa su ka kira, domin a tattauna matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

“To ya kamata a sani cewa kowane dan majalisa daga kowace jam’iyya akwai aikin da ya sha masa kai, ba shi ma da lokacin zama ya rika gulma ko tsugudidin bambance-bambancen siyasa.

Doguwa ya ce don haka surutan Elumelu ba gaskiya ba ne, sun fi kama da tatsuniya ko zuki-ta-malle. Kawai dai ya na burga ce da ci-da-buguzum, saboda matsalar da ke gaban su ta sha masu kai, sun rasa mafita, shi ne ya ke yin ki-fadi.

Doguwa na sanar da ‘yan APC cewa babu wani mai sha’awar komawa PDP kuma kowane dan APC ya bakin kokarin sa wajen ciyar da jam’iyya da kasa a gaba.

Share.

game da Author