Ni da Obasanjo mu ka kubutar da dalibai 27 na Babbar Kwalejin Gandun Daji ta Afaka – Gumi

0

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rawar da shi da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo su ka taka wajen kubutar da daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Gandun Daji da ke Afaka, cikin Jihar Kaduna.

Masu garkuwa sun sako dukkan daliban 27 a ranar Laraba, bayan sun shafe kwanaki 55 a tsare.

Tun da farko dai dalibai 37 ne aka yi garkuwa da su, amma wasu sun kubuta.

Masu garkuwa sun nemi a biya su naira miliyan 500, amma Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ba za ta biya ko sisi ba, kuma ba za ta tattauna da ‘yan bindiga ba.

Sai dai har yanzu ba a sani ba ko gwamnatin Kaduna ta biya kudi ko kuma da hannun ta wajen tattauna sakin daliban ko babu.

Amma dai Kwamishinan Harkokin Tsaro, Samuel Aruwan ya tabbatar da an sako daliban da su ka rage din su 27.

Amma jaridar Daily Nigerian ta buga cewa an yi musayar wani fursunan dan bindiga da gwamnati da aka tsare, kafin masu garkuwar su amince su saki daliban da su ke tsare.

Daily Nigerian ta ce sakin dan bindigar na daya daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Gumi da Obasanjo, kafin su shawo kan masu garkuwar su amince su saki daliban.

Jaridar ta kuma kara da cewa iyayen daliban sun biya diyya, kamar yadda wata majiya daga cikin jami’an tsaro ta shaida masu.

Jaridar ta ce majiyar na daga cikin bangaren masu tattaunawar.

Bayanin Sheikh Gumi:

A ranar Alhamis iyayen daliban da aka sako sun kai wa Gumi ziyarar yi masa godiya dangane da rawar da ya taka wajen kubutar da ‘ya’yan su.

A wurin ne Gumi ya yi bayanin irin kokarin da shi da Obasanjo su ka yi wajen ceto rayukan daliban.

“Rawar da ni da Obasanjo mu ka taka wajen kubutar da daliban Afaka su 27, aikin mu kawai shiga tsakani ne. Saboda ba da mu ‘yan bindiga ke fada ba. Da gwamnati su ke fada.” Haka jaridar Punch ta ruwaito Gumi ya fada.

Shirin Da Mu Ka Gano ‘Yan Bindiga Na Kullawa -Gumi:

“To sai mu ka gano ‘yan bindigar nan sun shirya rika kai wa gwamnati hare-hare, ta hanyar kutsawa makarantun gwamnati su na kwasar yara.

“Da mu ka gano haka, sai mu ka yanke shawarar cewa ba za mu saduda mu rike hannaye su yi tsaye, mu zuba ido haka na faruwa ba. Sai mu ka ce gara dai mu tashi tsaye mu shiga mu fita mu shiga tsakanin tattauna sakin wadannan yara da ke hannun su. To kuma hakan mu ka yi bayan mun sha fama da fadi-tashi.

“Amma dai daga karshe, an cimma matsaya, kuma an sako yaran. Saboda haka mu na murna dukkan su sun tsira ba a kashe ko daya daga cikin su ba.”

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta yi kokarin jin ta bakin Obasanjo, amma kakakin yada labaran sa Kehinde Akinyemi ya yi alkawarin kiran wakilin mu idan ya kimtsa, sai dai har zuwa lokacin buga labarin bai kira ba.

Wadannan dalibai 27 da aka kubutar, daban su ke da wasu 16 na Jami’ar Greenfield ta Kaduna, wadanda har yanzu ke a hannun wasu ‘yan bindigar daban.

Tuni dai wadannan hatsabiban ‘yan bindiga su ka kashe wasu daga cikin su, kuma su ka yi barazanar karasa kashe sauran idan ba a biya su kudin fansa ba.

Bayan kwana biyu da cikar wa’adin biyan diyya ko su kashe su baki daya, har yau gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba.

Muna Kokarin Kubutar Da Daliban Jami’ar Greenfield – Gumi:

Sheikh Gumi ya ce su na tattaunawar shiga tsakani wajen kubutar da sauran daliban Jami’ar Greenfield ta Kaduna su 16 da ke hannun ‘yan bindiga.

“Mu na ci gaba da tattauna yadda za a kubutar da wadannan daliban jami’a. Kun san sun yi barazanar kashe su baki daya bayan cikar wa’adin da su ka bayar. Amma yayin da mu ka yi masu magana, sai su ka saurara tukunna.

“To godiyar mu a yanzu dai ita ce da su ka daina yi masu kisan dauki dai-daya. Saboda haka mu na ci gaba da tattaunawa da su. Ina kuma fatan a fahimci wannan kubuta da daliban Afaka su ka yi, ta nuna akwai yiwuwar tattaunawa da ‘yan bindiga a shawo kan su a kubutar da daliban.” Inji Gumi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito shi.

Share.

game da Author