Najeriya na kusa da yin tinkaho da Janar Attahiru kafin rasuwar sa – Inji Buratai

0

Tsohon Hafsan Hafsoshin Askarawan Najeriya, wanda marigayi Ibrahim Attahiru ya gada, Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa Attahiru ya rasu a daidai lokacin da ya kusa samun nasarar da Najeriya za ta yi tutiya da shi.

Buratai ya ce kwanan Attahiru ya kare a daidai lokacin da ya samo lagon yaki da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga a kasar nan.

Ya bayyana mutuwar Hafsan Hafsoshin Askarawan Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a matsayin babban rashi ga Najeriya, ‘yan Najeriya da duk wani mai son ganin zaman lafiya ya wanzu a kasar nan.

Buratai ya ce Attahiru da sauran manyan hafsoshin sojojin da hatsarin jirgin ya ritsa da su, sun yi wa kasar nan aiki tukuru.

Ya kara da cewa mutuwar su Janar Attahiru ta sosa masa rai matuka tare da girgiza shi, domin Najeriya ta yi babban rashin jan gwarzon da ke da kuzari da hobbasan kokarin ganin ya gaggauta samun nasara a dukkan yake-yaken da sojojin Najeriya ke yi a fadin kasar nan.

“A madadi na da iyali na, ina mika ta’aziyyar wannan babban rashi ga Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, iyalan mamatan, Babban Hafsan Tsaro, Babban Hafsan Sojojin Sama da daukacin manya da kananan hafsoshin sojojin Najeriya.”

Share.

game da Author