Wani likita dake aiki da asibitin ‘Obafemi Awolowo’ dake Ile-Ife, kuma shugaban gidauniyar ‘Chest Care Foundation’ Gregory Erhabor ya bayyana cewa mutum miliyan 339 na kamuwa da cutar Asthma duk shekara a duniya.
Erhabor ya kuma ce duk shekara cutar na kwantar da mutum sama da 500,000 a asibitoci sannan mutum 400,000 na mutuwa a dalilin cutar a duniya.
Bincike ya nuna cewa kafin nan da shekaran 2025 mutum miliyan 400 za su iya kamuwa da cutar a duniya saboda rashin maida hankali wajen kawar da cutar.
A Najeriya kuwa bincike ya nuna cewa mutum miliyan 13 zuwa 15 za su iya kamuwa da cutar duk da cewa akwai hanyoyin da za a bi domin hana mutane mutuwa a dalilin cutar.
Menene cutar Asthma.
Cutar Asthma cuta ce dake kama manufashin mutum inda a dalilin haka ake samun matsalar rashin mumfashi yadda ya kamata.
Alamun cutar
Alamun cutar Asthma sun hada da;
1. Ciwon kirji,
2. Rashin yin numfashi yadda ya kamata.
3. Tari
4. Yin numfashi da sauro.
5. Zuciyar mutum zai Riga bugawa da sauri.
6. Yawan jin kaikayi a mokogwaro.
Hanyoyin kamuwa da cutar
1. Yawan motsa jiki kamar su buga kwallo, gudu, tsalle da sauran su.
2. Shakar gurbatacciyyar iska.
3. Yawan shakar hayaki.
4. Kiba.
5. Yawaita shan magunguna kamar su Aspirin,Ibuprofen,Naproxen da sauran su.
6. Yawan damuwa.
7. Figiji ko tsoro.
8. Yawan kusantan dabobbi kamar kare ko mage.
9. Kin Shan magani a lokacin da aka kami da mura inda haka ke iya hangar da cutar.
10. Shakar iska mai sanyi kamar na ac sannan da yawan Shan ruwan sanyi musamman lokacin sanyi.
Hanyoyin guje wa kamuwa da Asthma
1. Zama cikin tsaftattacen wuri
2. Gujewa yawan shan magunguna ba tare da izinin likita ba.
3. Gujewa shakar gubataciyyar iska, kura da hayaki.
4. Shan maganin da ya kamata da zaran an kamu da mura.
5. A daina yawan damuwa.
6. A rage yawan kusantan dabobbi musamman kare ko mage.
7. A rage yawan Shan ruwan sanyi musamman lokacin zafi.
Discussion about this post