Muna taya iyayen daliban Jami’ar Greenfield fatan murmurewa daga tashin hankalin da suka shiga – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya aika da sakon taya murna ga iyaye dangi da ‘yan uwan daliban Jami’ar Greenfield da’ yan bindiga suka sako ranar Asabar.

Daliban sai da suka shafe kwanaki 40 tsare a hannun ‘Yan bindiga.

Sanarwar da gwamnan ya fitar a shafin Tiwita ranar Asabar, ya ce yana yi wa ɗaliban da danginsu fatan murmurewa daga tashin hankalin da suka shiga tare da sake jajantawa dangin waɗanda aka kashe.

“Gwamnatin Kaduna tana aiki da gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron mutanen jihar”.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da suka sace daliban jami’ar Greenfield dake kan titin Kaduna-Abuja, sun sako daliban.

Daliban su 17 sun shafe kwanaki 40 tsare a hannun ƴan bindigan.

Idan ba a manta ba, kwanakin baya iyayen daliban sun gudanar da zanga-zanga, suna roko da yin kira ga gwamnati su saka baki a sako daliban.

Sai dai kuma gwnatin jihar Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta ce biyan kudin fansa ba ya cikin tsarin mulkinta. Hakan ya sa iyayen daliban suka yi ta fitan kudade dumin maharan su saki daliban.

Shugaban ƴan bindigan ya bayyana a wata jawabi da yayi wa gwamnati da iyayen daliban cewa naira miliyan 55 ɗina suka aiko kudin fansa, sunnyi amfani ne sun ciyar da ɗaliban, sai sun kara aiko da naira miliyan 100 kafin su sake su.

Zuwa yanzu ba a samu wasu bayanai da ke nuna ko iyayen daliban sun kara aika wa ƴan bindigan kudi ko a’a.

Share.

game da Author