Mun maida wa jihar Delta kudin da Ibori ya sace a lokacin yana gwamna – Akanta-Janar

0

Akanta-Janar na Kasa Ahmed Idris, ya bayyana cewa gwamnati ta maida wa jihar Delta kudin ta wanda tsohon gwamnan jihar James Ibori ya sace daga asusun jihar a lokacin yana gwamnan jihar.

Kudin, Fam Miliyan 4.2 wanda aka dawo dasu daga kasar Birtaniya an ajiye su ne da farko a asusun gwamnatin tarayya.

Akanat Idris ya shaida wa mambobin kwamitin majalisa da ta gayyace shi ya yi mata bayani kan abinda ya sani game da kudin da aka kwato.

” Duk wani kudi da aka kwato su daga tsohon gwamna ana maida wa jihar kudin ta ne kai tsaye”

Sai dai kuma hakan ya sha bambam da kalaman ministan shari’a Abubakar Malami inda ya shaida a wata hira da yayi da BBC cewa ba za a biya kudin zuwa asusun gwamnatin jihar Delta ba, yace gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kudin ne wajen gyaran titi da sauran ayyukan ci gaban kasa.

Malami ya ce kudin sun zama na Najeriya ba na jihar Delta ba, saboda haka kasa za a yi wa aiki. Sai dai kuma masu yin fashin baki nuna rashin amincewar su da wannan kalaman Malami ba. Suna ganin tunda dai kudin jiha ce a maida wa jihar da aka sato su kudin su shine yafi dacewa.

Share.

game da Author