An damƙe Mashawarcin Musamman na Gwamnan Jihar Neja a Harkokin Kayan More Rayuwa, Yusuf Musa saboda hannun da ya ke da shi wajen haɗa baki a kwakkwance ƙarafunan titin jirgin ƙasa, wato layin-dogo.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, Bola Longe ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke wa manema labarai faretin barayin, a hedikwatar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, ranar Alhamis, a Lafiya, babban birnin jihar.
Cikin wata ƙarin waziƙa da ‘yan sandan su ka turo wa PREMIUM TIMES, an bayyana cikin waɗanda aka danƙe ɗin har da jami’an ‘yan sanda.
Sanarwar ta bayyana cewa an damƙe su ne bayan samun wasu bayaani na sirri da su ka samu kan abin da barayin ke aikatawa.
“Waɗanda aka kama ɗin sun maida satar kwangirin jirgin ƙasa tankar sana’a, inda su ke karaɗe yankunan da jirgin ƙasa ke bi zuwa Jihar Benuwai.
“Ganin yadda satar su ta addabi hukumar kula da hanyoyin jiragen ƙasa, sai aka kafa ƙaƙƙarfan kwamitin magance matsalar a lokaci guda.
“Ai kuwa shirin da aka yi masu ya biya bukata, domin a ranar 16 Ga Mayu, ds ranar 25 Ga Mayu, 2021, aka same su su na ta aikin haƙa da kwance kwangiri a kan hanyar Agyaragu Tofa cikin Karamar Hukumar Lafiya da kuma Angwan Alago, cikin yankin Kadarko a Ƙaramar Hukumar Keana.”
Ya ƙara da cewa an kama Sufeton ‘Yan Sanda Richard Joseph, Mali Peter, wani Saje da Ibrahim Usman jami’in NSCDC da wasu mutane uku duk aka damƙe su.
Ya ce da aka ƙara bincike ne aka kamo Musa da wasu barayin su10.
Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da wani tsohon kansila, Marra Thai, wani ɗan Chana mai suna Yong Xing, kuma Manaja na Yong Xing Steel Comoany, Tunga Maje, FCT Abuja. Sai Samuel Shagbaor, wani ma’aikacin Hukumar Jiragen Ƙasa.
Kwamishinan ya ce wani mai suna Abubakar Nuhu ya yi ƙoƙarin bai wa ‘yan sanda toshiyar bakin naira 160,000 don su saki kayan da aka kama.
Da manema labarai su ka tambayi Mashawarcin Gwamna, ya bayyana cewa shi babban ɗan kasuwa ne, ban san ƙarafan da na saya a wurin su cewa na sata ba ne.
“Bayan na saya, na sayar da su naira miliyan,3.6.” Inji Musa.
Discussion about this post