Marasa kishin Najeriya daga cikin malaman addini da ‘Yan siyasa ke neman wargaza kasar – Fadar Shugaban Kasa

0

Mai ba shugaban Kasa shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ya bayyana cewa gwamnati ta gano cewa akwai wasu marasa kishin Najeriya daga cikin Malaman addini da ‘Yan siyasa da suka lashi takobin tarwatsa kasar nan.

Ya ce shirin wadannan marasa kishin kasa shine duk kasa ta dagule, yadda dole sai an yi juyin mulki ko ta halin kaka.

Wannan shirin ba wai a kasa Najeriya kawai ake shiya shi ba, har da hadin kan wasu kasashen waje kuma abinda suke so shine su yamutsa kasar, komai ya dagule daganan sai ko ta halin kaka a yi juyin mulki.

” Mun gano cewa wasu daga cikin irin wadannan shugabanni sun fara yada manufar su da kokarin shirya gagarimin taro da gangami inda anan ne za a amince gaba daya cewa cewa gwamnatin Buhari ta gaza. Sai kuma kasa ta dau zafi an shiga cikin rudani. Wannan shine burin su. kuma tuni har sun fara tuntubar juna.

Gwamnati ta gano shirin su. ‘yan Najeriya sun zabi gwamnatin da suke so wanda za ta ci gaba da mulki daga nan zuwa 2023. Duk wani abu da ba haka ba ‘yan Najeriya ba za su amince da shi ba. Kokarin gwamnatin shine ta tabbatar da ana ci gaba da samun hadin kai a fadin Kasar nan.

Share.

game da Author