Manoman dawa a Najeriya sun fito da dabarun rage dibga asara bayan sun yi girbi

0

Ganin yadda Gwamnatin Najeriya ba ta maida hankali wajen bunkasa noman dawa, duk kuwa da cewa abinci ce ita mai gina jiki, sai manoman dawa su ka bijiro da dabarun saukake yawan asarar da su ke dibgawa bayan sun yi girbi.

Ba mutane kadai ke cikin dawa ba, ana amfani da ita a matsayin abincin dabbobi da sauran sinadarai masu tarin yawa.

Daya daga cikin matsalolin da manoman dawa ke kuka da ita, akwai rashin ingantaccen wurin ajiya bayan an girbe dawa daga gona. Sannan kuma beraye da tsutsotsi kan yi masu barna sosai. Saboda gwamnati ba ta tallafawa wajen bunkasa noman dawa, sai manoman ta su ka fito da ta su dabarar.

Wani hamshakin manomin dawa mai suna Atrogor Ijeh da ke Cross River, ya bayyana yadda su ke gaganiyar kulawa da adana dawar su domin su samu damar ci gaba da hada-hadar noman na dawa.

“A baya mun shafe shekaru da yawa beraye da burgu na yi mana barna bayan mun yi girbin amfanin gona. Amma yanzu an fito da dabara tsakanin da jami’an karamar hukuma da mu manoma.

“A da tun daga gona za mu yi sussuka mu sheke. Kuma masu aiki majiya karfi ake sawa su cashe, su sheke sannan a zuba cikin buhunna. Amma yanzu sauki ya samu saboda ta hanyar kungiya an samar mana injinan casar dawa a saukake. Hakan kuma ya rage asarar da ake samu idan majiya karfi ne su ka yi casar da kan su.

Shi ma wani mai suna Goni Adam, da ke noman dawa a Jihar Barno, kuma Shugaban Masu Noman Dawa na Jihar Barno (NASPPAM), ya shaida wa wakilin mu cewa duk da rashin tsaro da hare-haren ‘yan ta’adda, ba su hana sun riba ba, wato ba su tabka asara ba.

“Mu na da dumbunan ajiyar dawa a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.

Shi kuwa Ibrahim Yusuf mai Auwzak Farms, wanda ya shafe shekaru 30 ya na harkokin noman dawa, cewa ya yi saboda rashin wadataccen wurin adana dawa har tsawon wani lokaci, sai ya gwammace ya rika nike garin ya na maida shi abincin dabbobi.

Share.

game da Author