Majalisar Tarayya ta fara nazarin soke shirin yi wa kasa hidima na NYSC

0

Dan majalisan dake wakiltar jihar Ribas a majalisar tarayya, Awaji-Inimbek Abiante (PDP) ya mika wata kudiri da ke neman a soke shirin yi wa kasa hidima wanda dalibai da suka kammala karatun jami’a ke yi.

Abiante ya ce NYSC ba shi da tasiri kuma yanzu musamman halin da kasa ta fada ba tun yanzu ba.

” Wannan shiri na bautar Kasa, ko kuma yi wa kasa hidima ya yi tsufan da ba shi da amfani a kasa yanzu. Tashin hankali ne kawai ya ke saka iyayen yara.

” Ba ya ga saka yayan mutane cikin hadari, sannan kuma ya sa ma’aikatu da dama ba su daukan ma’aikata sai su jira duk shekara idan aka turo yan bautan kasa sai su kwashe su suna biyan su kudi kalilan suna musu aikin jaki.

” Wani abu kuma da ya sa dole a sake lale game da wannan shiri na bautar kasa, wato yi wa Kasa hidima, NYSC shine yadda wuraren horas da daliban ya ragwargwabe, ba su samu kula.

A karshe ya ce ainihin makasudin kirkiro da tsarin yanzu ba shi da tasiri. Maimakon haka a kirkiro da abinda za arika taimakawa matasa ne, wanda za su mfana dashi kaitsaye bayan sun kammala karatu ba karauniyar bin hanya ba da sunan bautar kasa.

Share.

game da Author