Majalisa za ta bijiro da dokar haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa

0

Yayin da akasarin wadanda aka fi yin garkuwa da su duk wadanda ake wa takakkiya har kauyuka a gudu da su ne, sai kuma wadanda ba su iya karakaina a kan jiragen sama, Majalisa za ta bijjro da dokar haramta biyan masu garkuwa fansa.

Kudirin dokar wanda ya tsallake karatu na biyu a gaban Majalisar Dattawa, ya bijiro da haramta biyan masu garkuwa diyyar sako wanda aka kama.

Kuma ya hana biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga da Boko Haram.

Wannan doka za ta bijiro da tsatsauran hukunci ga duk wanda aka kama yana hada baki da masu garkuwa ko ‘yan bindiga ko Boko Haram.

Sanata Francis Onyewudi, dan PDP daga Jihar Imo ne ya gabatar da kudirin, wanda tun a ranar 1 Ga Maris aka yi masa karatu na biyu.

Idan har kudirin ya zama doka, to zai canja Sashen Doka na 14, wanda idan aka yi masa kwaskwarima, zai rika daure duk wanda aka samu ya biya kudin fansa ko ya hada baki da ‘yan bindiga ya karbi kudin fansa har daurin shekara 15.

Yayin da su ke ganin idan aka daina biyan kudin fansa, za a samu saukin garkuwa da mutane, sanatocin sun kuma yi kira ga jami’an tsaro su sake tashi tsaye wajen ganin sun hana garkuwa da jama’a a sassa daban-daban na Najeriya.

Share.

game da Author