KYAN DAN MACIJI: An damke matashi da sabbin wayoyin sata guda 273, na naira miliyan 15 a Katsina

0

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta damke wani matashi mai suna Lawal Ibrahim da wayoyin sata har guda 273.

An kiyasta kudaden wayoyin a jimlace za su kai naira miliyan 15, wadanda ya fasa wata mota ya sace.

Kakakin Yan sandan Katsina Gambo Isah, ya bayyana cewa Ibrahim Lawan mazaunin unguwar Fegi ne da ke cikin Daura, ya fada wata mota ce ya kwashe wayoyin.

Lawan dan shekaru 23, ya saci wayoyin ne a ranar 22 Ga Afrilu, amma bayan an bi sawu, sai jami’an tsaro su ka yi nasarar damke shi tare da wayoyin da ya sata din.

“Lawan tantirin barawo ne, an fi sanin sa da lakabin ‘Abba Kala’ ko Abba Swags, kuma ya taba zama gidan kurkuku.

Abba Kala ya kware wajen haura gidajen mutane da satar babura.” Inji ‘Yan sanda.

“Ranar Abba Kala ta baci a lokacin da ya shiga gidan wani mai suna Kamalu Ibrahim, mai shekaru 33 a Shagari Low Cost, Daura, ya fasa mota kirar BMW, Mai amba JW 01 DRA, ya saci wayoyin.

“Binciken da mu ka yi an gano dukkan wayoyin da ya sata. Kuma da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da shi a gaban mai shari’a, domin a hukunta shi.”

Share.

game da Author