Kwangila Mbaka ya nema bai samu ba, sai ya huce kan Buhari – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta yi zargin babu wani dalilin da Babban Limimin Kirista dan Enugu, Ejike Mbaka ya sa ya ragargaji Buhari, sai don kawai ya nemi kwangiloli bai samu ba.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a, ya ce wannan shi kadai ne dalilin fushin da faston ke yi.

Mbaka wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015 da 2019, a yanzu kuma ya nemi Buhari ya sauka ko kuma a tsige shi, saboda ya kasa samar da tsaro a kasar nan.

Sai dai kuma Fadar Shugaba Buhari ta ce Ejike ya huce haushi ne kan Buhari, saboda ‘ya nemi a saka masa goyon bayan da ya yi wa Buhari.

“Wanda bai san abin da ake ciki ba zai yi mamaki idan ya ji Father Mbaka ya dawo a yanzu kuma ya na sukar Shugaba Buhari.

“To gaskiyar lamari shi ne, Mbaka ya nemi ganin Shugaba Buhari, kuma Fadar Shugaban Kasa ta shirya masa ganawa da shi.

“Amma abin mamaki da daure kai, da ya tashi zuwa, sai ya zo da wasu jami’an kamfanonin neman kwangila daga kamfanoni uku.

“Da su ka gana da Buhari, mamaki ya cika Shugaban Kasa, yace to ya je a bi duk wata ka’idar da ake bi, domin shi ba ya bada kwangila.

“To haushin Mbaka bai samu kwangila gaba-dadi ba, sai ya dawo yanzu ya na caccakar Buhari.

“Da ya ke ba al’adar Fadar Shugaban Kasa ba ce ta fallasa wasu abubuwan da aka yi a cikin sirri, shi ya sa ba za mu fito da hotunan zuwan Mbaka Fadar Shugaban Kasa ba. Amma idan aka fito da hotunan, za a sha mamakin ganin tawagar neman kwangilar da Mbaka ya je da ita.” Inji Garba Shehu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin raddin da APC ta yi, inda ta ragargaji babban fasto Mbaka don ya ce Buhari ya gaza, ya sauka.

Jam’iyyar APC ta ragargaji babban limamin Kirista, Ejike Mbaka, wanda bayan ya shafe shekaru ya na goyon bayan Shugaba Muhamamdu Buhari, a wannan karon kuma ya kware masa baya, ya ce ba ya iya samar da tsaro a Najeriya, don haka ya sauka kawai.

APC ta ce kalaman da Mbaka ya yi amfani da su sun yi tsaurin da za su iya haddasa tarzoma a kassr nan.

Kakakin APC Yekini Nabena, ya yi barazanar kai karar Mbaka a Babban Cocin Katolika, idan ya ci gaba da kinkimo danyar magana ya na dankara wa Gwamnatin Tarayya.

Mbaka wanda shi ne Shugaban Cocin Adoration Ministry da ke Enugu, kwanan nan ya yi kira ga Majalisar Tarayya ta tsige Shugaba Buhari idan ya ki sauka saboda ya kasa samar da tsaro a kasar nan.

Mbaka dai ya yi wannan furuci a cocin sa, inda ya yi kira ga fadar shugaban Kasa ta gaggauta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Yekini Nabena ya ce kamata ya yi Mbaka ya maida hankalin da wajen ibada a cocin sa, maimakon ya rika tsoma baki cikin siyasa, wadda babu abin da ya sani a cikin ta ko a wajen ta.

Ya kalubalanci Mbaka ya yi amfani fa cocin sa wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya a kasar nan.

Ya nemi Mbaka ya yi koyi da Yesu Almasihu, wanda ya ce ya bi hukuma sau da kafa a rayuwar sa, har zakka ya rika biya.

Ya nemi Mbaka ya maida hankali a coci, ya kyale ‘yan siyasa su yi siyasar su.

Share.

game da Author