Kungiyar Kwadago ta fara yajin aiki a Kaduna

0

Kamar yadda kungiyar kwadago ta shirya, shugabanninta da mambobinta na kasa da jihar Kaduna sun fito zanga-zanga a jihar Kaduna.

Tun farko dai ƴan kungiyar sun yi tattaki da ofishin kungiyarta zuwa sakatariyar jihar Kaduna.

A sakatariyar, PREMIUM TIMES HAUSA ta ga daruruwar ma’aikata sun yi cincirindo a kofar shiga ma’aikatar an hana su shiga.

Daga bisa ni sai dunguma zuwa sakatariyar. A sakatariyar shugaban kungiyar Ayuba Wabba ya ayi jawabi ga ma’aikatan Kaduna.

A wannan jawabi, Wabba ya ce ba za su bari a na cin mutuncin ma’aikatan jihar Kaduna ba da sunan wai ana aiki ba.

” Wannan zanga-zanga muna yi ne don tilasta wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya dakatar da shirin sallamar ma’aikatan jihar Kaduna da ya kidiri yi.

Tuni dai ka daina siyar da man fetur, aka yanke samar da wutar lantarki a fadin jihar.

Daga sakatariyar jihar sai masu zanga-zangar suka dunguma kuma zuwa majalisar dokokin jihar Kaduna.

Share.

game da Author