Kungiya mai zaman kanta ta raba wa ‘yan mata audugar al’ada a jihar Kaduna

0

Kungiya mai zaman kanta ‘Eagle Lead Development Initiative (ELDI)’ ta raba wa ‘yan mata audugan al’ada a Unguwar Yelwa dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar Peter Ezekiel ya sanar da haka a hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Talata.

Ezekiel ya ce adugar na daga cikin tallafin da asusun UNFPA ta kawo Najeriya domin inganta fannin ilimi a kasar nan.

Ezekiel ya ce kungiyar ta wayar da kan ‘yan mata a Unguwar Yelwa hanyoyin gujewa kamuwa da cututtukan dake kama al’amurar mace musamman a lokacin al’ada sannan da yadda za su zubar da audugan da suka yi amfani da su.

Ya kungiyar ta yi hakan ne saboda mafi yawan ‘yan mata basu da masaniyar yadda za su kula da kansu a lokacin da suke al’ada da yadda za su zubar da audugar da suka yi amfani da shi.

A watan Yuni 2020 PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda likita akan dawainiyar haihuwa na mata, Abosede Lewu ta yi kira ga mata da su rage yawan shan magani dake rage laulayi a lokacin al’ada a cewa yin haka na lalata mahaifar mace.

Likitan ta ce yawan shan magani musamman ga budurwa wacce bata haihuwa ba a lokacin da take haila na iya hana haihuwa.

Lewu ta yi kira ga mata da su daina shan ire-iren wadannan magunguna domin kada ya illata su.

Hanyoyin rage laulayi da radadin al’ada ga mata

1. Motsa jiki; Ba sai mace ta tashi tana tsalle-tsalle ba ko kuma guje-guje ba mace za ta iya motsa jiki a cikin gidan ta ta hanyar aiyukkan cikin gida

2. Amfani da ruwan zafi; Da zaran mace ta fara al’ada ta rika wanka da ruwan dumi, sannnan ta rika shan shayi mai zafi.

3. Hutu kamar barci na rage ciwon kai da zazzabin da akan ji a lokacin haila.

4. Dabarun bada tazaran hihuwa; Wasu likitoci sun ce amfani da dabarun bada tazaran haihuwa zai taimaka wajen rage laulayin haila.

5. Cin wasu kayan abinci dake kara wa mutum karfin garkuwa; A lokacin da mace ta fara al’ada kamata ya yi ta rika cin kayan bincike dake dauke da sinadarin inganta garkuwan jiki.

Share.

game da Author