Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda shida a Karamar Hukumar Ini ta Jihar Akwa Ibom, a ranar Asabar.
Wani jami’in gwamnatin jihar da ba ya so a ambaci sunan sa, ya shaida wa wakilin mu cewa maharan sun kuma banka wa wani ssshe na ofishin DPO din Karamar Hukumar wuta.
“Sun tafi kai-tsaye inda gidajen kwanan ‘yan sandan su ke, su ka bude masu wuta nan take duk su ka mutu.” Inji majiyar.
Shugaban Karamar Hukumar Ini da Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Ini duk sun ziyarci wurin da aka yi kisan.
Kakakin ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, Odiko MacDon ya tabbatar da kisan da aka yi wa jami’an su, amma bai ambaci ko jami’in tsaro nawa aka bindige ba.
Ya kara da cewa cikin wadanda aka kashen, hat da wani dan sanda da matar sa.
Ba wannan ne karo na daya ko na biyu din kisan ‘yan sanda a Akwa Ibom cikin kwanaki 30 ba.
An Bindige ‘Yan Sanda Bakwai A Jihar Ribas:
A Jihar Ribas kuma an bindige ‘yan sanda bakwai a ranar Juma’a, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.
An bindige su ne a ofisoshin ‘yan sanda da ke Elimgbu da kuma Rumuji.
A jihar Ribas ma ba wannan ne hari ko kisan jami’an tsaro na farko ko na biyu a cikin wata daya ba.