KUDU TA DAGULE: An banka wa ofishin INEC wuta a Akwa Ibom, an cafke harsashen ‘mashin ga’ 753 a Ebonyi

0

Dandazon zauna-gari-banza sun banka wa Ofishin Hukumar Zabe ta Kasa wuta a jihar Akwa Ibom, a ranar Lahadi.

Lamarin ya faru a Karamar Hukumar Essien Udem, kuma INEC da jami’an tsaro sun tabbatar da cewa harin da aka kai wa ofishin shiryayye ne.

Kakakin Wayar da Kan Jama’a na INEC Festus Okoye ya tabbatar da an kai harin, cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Okoye ya ce Kwamishinan Zabe na Kasa na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini ne ya kai rahoton wutar da aka banka wa ofishin.

Sai dai kuma ya ce jami’in tsaron da ke kula da wurin ya tsere ba tare da samun wani rauni ba.

Daga cikin kayayyakin da aka kone akwai akwatinan zabe 345, ‘yan dakunan dangwala kuri’a guda 135, tankokin ruwa da kuma kujeru da tebura na cikin ofisoshi.

Okoye ya ce idan irin wannan tashe tashen hankula su ka ci gaba da afkuwa a kudancin kasar nan, to lamarin zai iya shafar zaben 2023 mai zuwa.

A jihar Ebonyi kuwa, ‘yan sanda sun cafke albarusai na babbar bindiga mashin ga har guda 753.

Kakakin ‘Yan Sanda na Kasa, Frank Mba ya sanar a ranar Lahadi cewa an kama albarusan a cikin buhu cikin wata motar haya da ta taso daga Abakaliki zuwa Umuahia.

Sannan rahotanni sun nuna a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, ana ci gaba da kai wa jami’an ‘yan sanda hare-hare.

Share.

game da Author