An sake banka wa wani ofishin INEC wuta a Jihar Imo, kwana ɗaya bayan banka wa wasu ofisoshin biyu wuta.
Wannan karo dai shi ne karo na takwas kenan ana ƙone ofishin INEC a Imo, tun bayan zaben 2019.
An ƙone ofishin ne da ke ƙaramar hukumar Njida, kwana ɗaya bayan an bindige Ali Gulak a Owerri, babban birnin Jihar Imo, kan hanyar sa ta tafiya filin jirgin Owerri, inda ya yi niyyar komawa Abuja a lokacin.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda aka banka wa kotuna da ofishin ‘yan sanda wuta a Imo, kafin kisan Ahmed Gulak.
Haka kuma wannan jarida ta buga labarin yadda aka kai wa ofisoshin INEC hare-hare sau 41 cikin shekaru biyiu, a faɗin ƙasar nan.
‘Yan bindiga sun bude wa tsohon Mashawarcin Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Ali Gulak wuta a Owerri.
An bindige Gulax mashawarci na Jonathan kan siyasa wuta ne a kan hanyar sa ta komawa Abuja daga Owerri.
Wani jigo a PDP, Umar Arɗo, ys buga a shafin sa na Facebook, inda ya tabbatar da mutuwar Gulak ta hanyar bindige shi da aka yi, kuma ya yi masa addu’ar neman rahama.
“Mun yi rashin ɗan’uwa kuma aboki, kuma ɗan jihar mu, Ali Gulak, wanda aka kashe a Owerri. Kafin kisan sa ya taba riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Jihar Adamawa, sannan tsohon Mashawarcin Tsohon Shugaban Kasa a Harkokin Siyasa.
“Allah ya bai wa iyalai, ‘yan uwa da abokan arzikin mamacin hakurin rashin sa. Shi kuma Allah ya gafarta masa.”
Gulak tsohon ɗan PDP ne, amma kafin zaben 2019, ya koma APC, kuma shi ne ya yi zaben-fidda-gwanin zaben Gwamnan Imo na 2019, wanda aka ce Hope Uzodinma ya lashe.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Imo, Elkanna ya tabbatar da kisan wanda aka yi wa Gulak.
Haka kuma ‘yan ƙungiyar IPOB sun tsame kan su daga zargi, IPOB ta ce babu hannun ta a ciki.
Kisan Gulak ya zo bayan an banka wa wasu kotuna wuta da kuma ofishin ‘yan sanda a jihar ta Imo.
Ofishin DPO na Atta da ke Ƙaramar Hukumar Njabane aka sa wuta.
Maharan sun riƙa ratattaka wuta kusan tsawon awa ɗaya, kafin su banka wa ofishin wuta.
Sun kuma banka wa Kotun Majistare da Babbar Kotu wuta a yankin. Kuma an ɗibga sata an kuma lalata kayyaki a wata cibiyar kula da lafiya da ke yankin.
Kakakin ‘Yan Sandan Imo, Bala Elkana ya tabbatar da hare-haren a Owerri, a cikin wata sanarwa da ya fitar.
An kuma banka wa wani ofishin ‘yan sanda na Orni da ke cikin Karamar Hukumar Owerri ta Arewa wuta.
An kai hare-haren a jajibirin dokar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya yi cewa kowa ya zauna a gida, kada ya fita.