Kotun Tarayya ta jaddada wa jihohi ‘yancin kafa dokar hana karakainar kiwon shanu

0

Babbar Kotun Tarayya ta jaddada wa jihohin Najeriya karfin ikon fara amfani da dokar haramta kiwon shanu sakaka a jihohin su.

Wannan matsayi da Babbar Kotun Tarayya, ta Abuja ta bayar ya dakushe kaifin bakin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, wanda ya furta cewa jihohin da su ka haramta kiwon shanu a cikin su, sun karya dokar Najeriya, domin ba su da ikon yin haka, tunda dokar kasa ba ta ba su ikon yi ba.

Babbar Kotun Tarayya a karkashin Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ce ta bayyana cewa jihohi na da ikon kafa dokar, tare da umartar ‘yan sanda su tabbatar ana bin dokar.

Ta yanke wannan hukunci ne a shari’ar da ta gudanar ta akwatin talbijjn din ‘virtual’, wato daga nesa.

An dai kai kara a gaban ta ne inda aka nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su rika tabbatar ana bin Dokar Haramta Kiwo da Kafa Garken Shanu ta Shekarar 2017, ta Jihar Bemuwai.

“Ni ina ganin babu bukatar ma a tilasta sai Shugaban Kasa ya tilasta jami’an tsaro. Domin lamari ne jihohin da abin ya shafa. Sai fa idan Shugaba ya ki bin tafarkin rantsuwar da ya yi shi ne wannan batu zai iya shigowa a ciki.”

Wani mai suna Mathew Nyutsa ne ya shigar da karar, inda ya nemi kotu ta jaddada ce a matsayin Shugaba da kuma rantsuwar da ya yi, to wajibin sa ne ya bi dukkan dokokin da tsarin mulkin kasa ya tanadar.

Sai ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ki bin umarnin dokar kasa, inda ya ki bi ko jadddada wa jami’an tsaro su tilasta bin Dokar Haramta Kiwo Barkatai da Kafa Mashekarin Shanu a Jihar Benuwai.

Mai shigar da kara ya yi wa kotu korafin cewa duk da Jihar Benuwai ta kafa dokar, har yanzu makiyaya na karakaina da shanu kuma su na kashe mutane a jihar Benuwai.

Sai dai Mai Shari’a Ojukwu ta ce, “tunda har Majalisar Jihar Benuwai ta sa wa dokar hannu, Gwamnatin Jihar Benuwai na da karfin ikon tilasta a bi dokar.

Share.

game da Author