Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 4 sun rasu sanadiyyar Korona ranar Talata a kasar nan.
NCDC ta kuma sanar cewa a wannan rana mutum 37 ne suka kamuwa da cutar a jihohi biyar da Abuja.
Jihar Legas wacce ta fi kowacce jiha a Najeriya yawan mutanen da suka kamu da cutar na da mutum 29, Akwa Ibom -3, Abuja -2, Gombe -1, Kaduna- 1 sannan Kano -1.
Zuwa yanzu mutum 166,098 suka kamu a kasar nan.
Mutum 2,071 sun mutu, an sallami mutum 156,528, sannan an yi wa mutum 2,093,243 gwajin cutar.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce an yi wa mutum 1,929,237 allurar rigakafin korona da ruwan maganin Oxford/AstraZeneca.
Kuma jami’an lafiya 440,000 aka yi wa allurar rigakafin korona zango na farko a kasar nan.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin neman wasu mutane har 90 da su ka kunshi Indiyawa 27 da ‘yan Najeriya 63, wadanda su ka shigo Najeriya ba tare da bin ka’idar tsayawa a killace su tsawon kwanaki bakwai ba kamar yadda dokar ta tilasta wa wanda ya shigo kasar nan daga Indiya, Brazil ko Turkiyya.
A ranar 1 Ga Mayu,2021 ne Kwamitin Dakile Cutar Korona ya sanar da sabuwar dokar cewa duk fasinjan da zai sauka Najeriya daga Indiya ko Brazil ko Turkiyya, tilas ne a killace shi tsawon kwanaki bakwai, kafin a bar shi ya shiga cikin garuruwan Najeriya.
Bijiro da wannan doka ya biyo bayan bullar sabuwar samfurin cutar korona mai yawan kisan mutane birjik musamman a Indiya da Brazil.
Wadanda Najeriya ke cigiya din su 90, an sanar cewa ba su bari an killace su tsawon kwanaki bakwai din ba, kuma tuni shige cikin garuruwan kasar nan, ana mu’amala da su.
Jami’an lafiya sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin dakile yaduwar cutar a kasar nan.
Discussion about this post