Shugaban Kwamitin dakile yaduwar Korona ta Kasa, Mukhtar Mohammed ya bayyana cewa daga daren Litini, gwamnati ta hana zirga-zirga da yawon dare a fadin kasar nan.
” Babu yawon dare daga karfe 12 na dare zuwa karfe 4 na safe. An saka wannan doka ne domin a dakile yaduwar Korona da take kunnu kai.
” Bayan hana yawon dare, an umarci gidajen holewa su ci gaba da zama a kulle. Haka kuma a rage yawan taruka zuwa mutum 50 kada ya wuce haka. Haka kuma ganawa da taruka na ma’aikatu, a ci gaba da yin su ta hanyar yanar gizo.