KORONA: Gwamnati ba ta saka sabbin dokokin dakile yaduwar cutar ba a Najeriya – Lai Mohammed

0

Ministan yada labarai kuma mamba a kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan dakile yaduwar Korona PSC, Lai Mohammed ya bayyana cewa ba sabbin dokoki gwamnati ta saka kan dakile yaduwar korona, jadda wadanda ke aiki a baya ne ta yi.

Ya ce abu sabo da gwamnati ta yi shine hana matafiya ‘yan Najeriya da suka ziyarci kasashen Brazil, Turkey da India shiga kasar nan ba tare da sun killace kansu na tsawon kwanaki 14 a gida ba.

“Gidajen holewa da kulub za su ci gaba da zama a rufe, ba za a yi taron da ya dara mutane 50 ba, mutum ba zai iya shiga ma’aikatu ko ofishin gwamnati ba tare da ya saka takunkumin fuska ba sannan gwamnati ta hana yawon dare daga karfe 12 na dare zuwa karfe 4 na asuba.

Mohammed ya ce gwamnati ta yi haka ne ganin yadda mutane suka ci gaba da harkokin rayuwar su ba tare da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da korona ba.

Ya ce irin wannan sakaci da mutane ke yi ka iya sa cutar ta kara barkewa a kasar nan a karo na uku.

Idan ba a manta ba kasar India ta yi irin wannan sakaci inda ta rika fada cewa ta kawar da korona daga kasanta.

A dalilin haka kuwa mutane suka ci gaba da gudanar da taro ana cudanya ba tare da ana kula ba.

Dalilin haka sai cutar ta sake barkewa a kasar inda a rana mutum 400,000 na kamuwa da cutar sannan mutum 4,000 na mutuwa a dalilin cutar a kasan.

Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin kare kansu da sauran mutane.

Share.

game da Author