A ranar Talata ne gwamnatin jihar Katsina ta karbi kwalaben maganin rigakafin cutar Korona na Astrazeneca Covid-19 domin fara yi wa mutane allurar rigakafin korona a jihar.
Gwamnan jihar Aminu Masari ya karbi kwalaben maganin rigakafin, mataimakin sa, shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar korona na jihar Mannir Yakubu da sauran jami’an gwamnatin jihar.
Da yake jawabi a wurin kwamishinan lafiya na jihar Nuhu Yakubu-Danja ya bayyana cewa mutanen da za a yi wa allurar rigakafin zango na biyu sune wadanda suka yi makonni 6 zuwa 8 baya sun yi musu allurar rigakafin a zangon farko.
Yakubu-Danja ya ce jihar ta yi wa mutane 52,580 allurar rigakafin korona a zangon farko a jihar.
Ya kuma ce gwamnati ta yi wa maniyyata aikin hajji 200,021 allurar rigakafin cutar a jihar.
Ya yi kira ga wadanda suka yi allurar rigakafin a zango na farko da su hanzarta kai kansu a yi musu allurar rigakafin zango na biyu domin samun kariya daga kamuwa da cutar Korona.
Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa Najeriya za ta fara yi wa mutane allurar rigakafin Korona karo na biyu a kasar nan.
Ya ce wadanda suka yi allurar rigakafin da farko ne za su dawo a yi musu allurar a karo na biyu.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kara yawan kwanakin da mutum zai jira bayan ya yi allurar rigakafin cutar na farko daga makonni 12 zuwa tsakanin makonni 6 zuwa 12.
Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum 1,690,719 allurar rigakafin a zangon farko.
Discussion about this post